‘Yan Boko Haram sun harba rokoki a Gamboru-Ngala, sun yanka mutane a Shiroro.
Mazauna Gamboru-Ngala da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru sun sanar da BBC cewa mayakan Boko Haram sun kai wasu hare-hare a garin nasu cikin dare zuwa safiyar Litinin.
Wani mazaunin garin da harin ya rutsa da shi ya ce sun ji karar harbe-harbe a wajen garin da tsakar dare kuma daga baya sai suka ji karar wasu abubuwa masu fashewa.
“Abin da ya faru shi ne jiya wajen karfe 12 da minti 5, mun ji karar harbin bindiga ko’ina cikin garin Gamboru-Ngala kusa da makarantar firamare da ake kira Central Primary School. Akwai wani sansanin jami’an tsaro haka a cikin makarantar.”
Ya ce baya ga harbe-harben, maharan sun harba rokoki cikin makarantar.
“An kai musu hari kuma an kone wannan makaranta, kuma an jefa roka cikin garin wanda ya kashe wani dattijo bayan da rokan ya fada cikin gidansa, sai dai sauran iyalansa sun tsira da rayukansu.”
Mazauna garin sun sanar da BBC cewa kafin sallar Azahar za a yi jana’izar dattijon, kuma an tafi da mutanen da suka samu raunuka asibiti domin a yi musu magani.
Ya kuma ce jami’an tsaron da ke zama a sansanin sun hada da sojojin Najeriya da kuma ‘yan sanda. Sansanin na kudu da garin na Gambobu-Ngala ne.
A cikin makon jiya ne gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kai wata ziyara ta musamman garin na Gamboru, inda ya kaddamar da wasu ayyuka, ciki har da bude hanyar da ta taso daga garin zuwa Maiduguri ta garin Dikwa.
Gwamnan ya kuma kaddamar da wani shiri na inganta tsaro, wanda a karkashinsa aka samar da karin jami’an tsaro.
Sai dai da alama wannan matakin bai wadatar ba, ganin yadda wadannan maharan suka iya kutsawa kusa da garin, kuma suka iya yi wa sansanin jami’an tsaron Najeriya mummunar illa.
“Gaskiya mun ji ba dadi. Muna cewa abin ya wuce ganin yadda aka bude mana hanya. Har muna cewa babu sauran Boko Haram a yankin namu. Kwatakwata ba mu yi tsammanin wannan abin zai iya faruwa ba. Mun sha wuya jiya a cikin garin Gamboru,” a cewar wani ganau.
BBC ta yi kokarin tuntubar kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu kan wannan harin, sai dai har zuwa lokacin da muka wallafa wannan rahoton, bai amsa kiran da muka yi ma sa ba.
Amma zuwa wayewar garin yinin Litinin, yawancin mazauna garin na Gamboru-Ngala na nan cikin garin.
Wani rahoton kuma na cewa da wayewar gari, daliban makarantar firamaren da aka kona sun fita zuwa makarantar, inda suka bukaci a bari su shiga makarantar domin su dauki darussa. Sai dai saboda hatsarin da ke tattare da yin haka, jami’an tsaron sun hana daliban shiga makarantar.
Da alama lamarin ya lafa, domin wata majiya a garin ta ce mazauna garin sun fita zuwa harkokinsu na yau da kullum.
- ‘Boko Haram ta mamaye garuruwa da dama a Neja’
- An haramta sayar da ‘Boxer’ da ‘Jingchen’ da wasu nau’in babura a jihar Neja
- IS ta fitar da wani bidiyo da ya nuna harin da ta yi iƙirarin kai wa a Buratai
An kona Galadiman Kogo a Jihar Neja
Mazauna garin Galadiman Kogo a jihar Neja da ke yankin arewacin Najeriya sun kwana a daji bayan harin da mayaka suka kai kan garin kuma suka kona kusan dukkan muhalan da ke cikinsa kurmus.
Wasu mazauna garin sun sanar da BBC cewa bayan da suka sami labari cewa maharan na kan hanya, sai ilahirinsu suka tsere cikin dare, inda suka bar dukiyarsu da gidajensu babu masu kula da su.
Wani ganau ya shaida wa BBC cewa “abin da ke faruwa, tun karfe 1 na dare zuwa karfe biyar na safiyar yau Litinin, ‘yan ta’addan nan na ciin garinmu, kuma sun kone mana duka gidajenmu. Wani gidan na shi ko an ba shi miliyan dari nawa ne ba zai iya sake gina gidan ba. Ba zai iya dawo mai da abin da ya yi asararsa ba.”
Mazauna garin da aka fi sani da Gal-Kogo sun kuma ce maharan sun kashe wasu ‘yan garin da ba su iya tserewa ba.
“Sun yanyanka wasu mutanen da suka tarar a cikin gidajensu,” in ji wani wanda lamarin ya shafa.
A halin yanzu mazauna garin na Galadiman Kogo na gudun hijira a wani sansani da ke cikin karamar hukumar Shiroro, inda suka ce suna zaune ne a filin Allah domin babu wanda ya basu matsuguni.
“Ga mu nan matanmu da ‘ya’yanmu suna ta kuka. Kukan ma dole a zo a bari domin ba shi da wani amfani,” in ji wani cikin mazan da ke neman mafaka a sansanin da suka taru, kamar yadda ya ce, tun da an riga an kona garin nasu.
Baya ga mutanen garin da ‘yan bindigan suka kashe, mutumin ya kuma ce wasu jami’an hukumar tsaro ta civil defence sun halaka bayan da motar da suke ciki ta taka wata nakiyar da maharan suka dasa a kan hanyar zuwa garin na galadiman Kogo.
“Sun sa bom a kan hanyar Power House, kuma ya tashi da motar, mutanen da ke ciki sun yi fata-fata.”
Mazauna wannan gari sun kuma ce an kai wata guda suna kokawa ga hukumomi kan hatsarin da suke fuskanta, amma a cewarsu, babu wani mataki da gwamnatin jihar ta Neja ta dauka.
“Gwamna Abubukar Lolo bai turo jami’ansa su ga halin da muke ciki a Galadiman Kogo ba, kuma gaskiya mun yi Allahwadai da wannan mulkin na shi.”
BBC ta yi kokarin jin ta bakin sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Matane domin jin ta bakin gwamnatinsa kan wannan harin da aka kai Galadiman Kogo, sai dai bai amsa kiran da aka yi ma sa ba.