An rawiato labarin mutumin da ya hadu da bacin rana inda ya yi asarar zunzurutun kudi har N200,000 a wajen buga caca.
Mutumin ya yanke jiki ya fadi sumamme a bakin shagon gidan cacan domin dai rancen kudin ya yi kuma gaba daya ya rasa su.
Jama’a a shafukan soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu, inda wasu suka dunga zolayar mutumin.
An tattaro cewa mutumin ya ari kudi N200,000 sannan ya yi amfani da shi wajen buga caca, amma abun bakin ciki sai ya sha kaye inda ya rasa komai.
”Wa ya kara wannan wakar, kwata kwata wannan mutumin ba zai ji kamshin lahira ba balle har ya shiga.”
jamoblaq77 ya ce: “Zai tashi anjima ku kyale shi watakila ya zata mafarki yake yi”
__h.o.I.u.w.a_s.e.u.n_ ya ce: “Su mayar mai da 50k don ya sake buga wani”
A wani labari na daban, cocin Omega Power Ministries (OPM) ya sake ceto wani matashi mai fama da nakasa sannan ya sanya farin ciki a zuciyarsa ta hanyar bashi tallafin karatu a kasar waje.
Bidiyon wani matashi mai kafa daya yana aiki a wajen gini ya yadu a shafukan soshiyal midiya kuma hakan ya burge mutane da dama.
Daya daga cikin wadanda bidiyon ya burge shine shugaban OPM Apostle Chibuzor Gift Chinyere wanda ya bayar da cigiyar mutum ya kuma gano shi.
Source:legithausang