Yadda ‘Yan Jagaliyar Siyasar Dan Majalisar Tarayya Daga Jihar Borno, Saleh Satomi Suka Ci Zarafin Wata Matashiya
A bidiyon an ga yadda matasa ‘yan bangar siyasar suka di ga dibgawa matashiyar mai suna Fadila Abdulrahman duka da ruwan ashariya bisa kabulantar dan majalisar da ta yi a siyasance a shafin ta na sada zumunta.
Baya ga dukan da ‘yan jagaliyar suka yi mata sun kuma farfasa wurin da matashiyar take sana’a.
Mahaifiyar Haneefa Da Aka Yiwa Kisan Gillah Ta Farmaki Makashin ‘Yarta
Rahotanni sun nuna cewa tuni dai Gwamna Zulum ya bada umarnin a zakulo matasan da suka ci zarafin matashiyar bisa bambancin ra’ayi na siyasa. Inda wasu kuma suke yin kira ga hukuma da su gayyato dan majalisar domin wanke kansa daga aika-aikar da ‘yan jagaliyar nasa suka yi.