Jihar Katsina – A kalla mutane uku ne wasu da ake zargin yan bindiga ne suka bindige har lahira a karamar hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina.
Vanguard ta kuma rahoto cewa an bindige wani mutumin a kafa yayin da yan bindigan sun sace wata mata mai suna Hawau Yusuf mai zaune a Unguwan Makeran jihar ta katsina.
Wani mazaunin garin, Marwan Zayyana, wanda ya tabbatarwa Vanguard lamarin, ya ce maharan sun kai hari garin ne misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin, a kan babura, suka rika cin karansu ba babbaka har 4.30 a garin.
Marwan ya bada sunan wadanda aka kashe din kamar har; Aminu Abdulwahab, Musa Abubakar da Sadiq Lawal.
Yayin da Sadiq Lawal an kashe shi ni cikin gidansa a Unguwan Tsugune, Abubakar an kashe shi ne a gaban gidansa a Unguwan Jageme.
Na uku shi kuma an kashe shi ne a gonarsa yayin da ya ke tserewa daga maharan.
A baya-bayan nan ana yawan kawo mana hari.
Mako daya da wuce, yan bindiga sun kawo mana hari misalin karfe 2.30 suka sace mutum shida.
Har yanzu suna hannunsu a daji.
“A ranar Lahadi ma, an sace wani matashi har yanzu ba a sako shi ba. Jiya, Litinin tsakanin karfe 4-4.30, bata garin sun kawo hari kuma sun kashe mutum uku. ”
”Bayan mutum ukun da suka kashe, ba a basu damar sun yi sata ba domin matasan garin sunyi kokari sun fattake su,” in ji Marwan.
Martanin yan sanda Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya ce bai riga ya samu rahoton ba, ya yi alkawarin zai bada bayani da zarar ya samu rahoton.
‘Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane.