Wannan dan Bindiga ne da aka kama yayin da yake shirin karbar kudin fansa a jihar Bauchi.
Kakakin ‘yansandan jihar, Ahmad Wakili ya bayyana cewa, wanda aks zargin, Ya’u Haruna ya sace Musa Adamu wanda ya nemi kudin fansa Miliyan 8.
Yace amma an samu bayanan sirri akan mutumin inda aka kamashi yana shirin karbar kudin fansa.
Tuni wanda aka kama din ya amsa laifinsa. Saidai kakakin ‘yansandan yace har yanzu suna kan bincike.