Iyalai, ‘yan uwa da abokan arzikin sojojin da suka rasa rayukansu sun zubda hawaye sai dai buhari bai samu halarta ba.
Sun hallara a Abuja inda aka yi jana’iza a masallacin kasa kafin a garzaya makabarta domin birnesu.
Sai dai shugaban kasa Buhari da Yemi Osinbajo basu samu halarta ba duk da babu dalilin yin hakan da suka bayyana Iyalai, ‘yan uwa da masoyan marigayi shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran sojojin da suka rasu a hatsarin jirgin sama na Kaduna a ranar Juma’a sun je jana’iza tare da taya makokin mutuwar da aka yi har zuwa makabartar sojoji.
Hatsarin jirgin saman wanda ya lakume rayukan dakarun sojin, ya auku ne saboda yanayin gari mara kyau bayan jirgin yayi yunkurin sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na farar hula dake Kaduna.
Matar shugaban sojin Najeriya da ‘yan uwansa, masoya da abokan arziki sun kasa boye tashin hankalinsu yayin da ake birne dakarun, Daily Trust ta ruwaito.
An biirnesu bayan jana’izar da aka yi a masallacin kasa da kuma addu’o’in da aka yi a cocin NAF, bayan dauko gawawwakinsu da aka yi daga Kaduna inda suka sauka filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari har mataimakinsa Yemi Osinbajo basu samu zuwa jana’iza ko birne zakakuran sojin ba duk da babu dalilin rashin zuwan nasu. Amma kuma Buhari ya samu wakilcin ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi wanda ya tsaya har aka birne marigayi Attahiru da sauran sojojin a madadin shugaban kasan. Buhari yace marigayin shugaban sojin kasan Najeriya zakakurin soja ne da ya sadaukar da rayuwarsa wurin bautawa kasa, ya rasu a lokacin da aka fi bukatar aikinsa.
A wani labari na daban, sojoji sun rufe yankin da jirgin dakarun sojin saman Najeriya yayi hatsari a ranar Juma’a a filin suaka da tashin jiragen sama na Kaduna.
Jirgin saman wanda ke dauke da shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji ya fadi a filin jirgin inda ya kashe dukkan mutum 11 da ke ciki har da matukan jirgin. A yayin jawabi kan lamarin, manajan filin jirgin sama na Kaduna,
Amina Salami ta sanar da Channels TV cewa hukumar sojin Najeriya sun mamaye yankin da lamarin ya auku.