Kungiyar tuntuba ta arewa a Najeriya ta yi kira ga ‘yan arewa da su kauracewa zuwa yankin kudanci domin Akwai matsala.
Kungiyar ta bada shawari kan yadda tafiyar ya kamata ta kasance idan ta zama dole sai an yi.
Hakazalika kungiyar ta bayyana yadda lamarin tsaro ya lalace a yankin kudanci musamman kudu maso gabas Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta gargadi ‘yan Arewa idan akwai shirin tafiya zuwa yankin Kudu maso Gabas a yanzu saboda halin da ake ciki na rashin tsaro.
Ta ba da shawarar cewa idan tafiyar ta zama dole, to ya zamana akwai jami’an tsaro a ciki, Nigeria Tribune ta ruwaito. Wannan ya na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban ACF na kasa, Cif Audu Ogbe, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce ta lura da yadda damuwa ta yi yawa game da hare-hare da kisan ‘yan Arewa mazauna da kuma maziyarta a yankunan Kudu, musamman Kudu maso Gabas.
Wani yankin sanarwar na cewa: “Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) a yanzu tana ba da kyakkyawar shawara ga duk ‘yan arewa da ke da niyyar zuwa Kudu maso Gabas.
“’Yan Arewa su auna muhimmanci da wajibcin irin wadannan tafiye-tafiye. Sai dai idan irin wadannan tafiye-tafiye suna da mahimmanci kuma suna da yanayi na tilas, kamar al’amuran rayuwa da mutuwa, sabanin haka bai kamata a yi su ba.”
”Kuma idan tafiyar ta kama dole, matafiyi ya dauki duk matakan tsaro a cikin zirga-zirgarsa yayin da yake can, gami da cudanya da jami’an tsaro a wuraren zama/wuraren da za a ziyarta.”
Lamurran tsaro na kara tabarbarewa a yankunan kudu, musamman yankin kudu maso gabas, lamrin da ya kai da zubar da jinane da dama ciki har da na wani gogaggen dan siyasa, Ahmed Gulak a karshen makon da ya gabata. Jaridar Cable ta ruwaito yadda wasu tsagerun ‘yan ta’adda suka hallaka Ahmed Gulak akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama a garin Owerri ta jihar Imo aranar Asabar.
A wani labarin na daban, Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya ce wadanda ke neman a soke shirin yiwa kasa hidimi na NYSC ba sa nufin Najeriya da alheri. Ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin wasu zababbun mambobin NYSC na rukunin ‘A’ diba na 2 da aka tura jihar Sokoto a fadarsa da ke Sokoto,
Daily Trust ta ruwaito. Maganar ta sarkin Musulmi martani ne ga yunkurin majalisar wakilai na soke shirin NYSC kwata-kwata a kasar duba da wasu dalilai da suka bayyana, jaridar Punch ta ruwaito.