Jami’ar Taraiya ta Lafia (FULafia), a Jihar Nassarawa, ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai ta guda 4.
Shugaban Sashin Hulɗa da Jama’a na Jami’ar, Abubakar Ibrahim, shine ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya yabawa manema labarai a jiya Juma’a a Lafia.
Ibrahim ya baiyana cewa an ɗauke daliban tun ranar Alhamis a Mararraba, wata unguwa ce kusa da jami’ar da misalin ƙarfe 11:30 na dare.
Ya kuma shaida cewa Shugaban Jami’ar, Farfesa Shehu Abdulrahman ya girgiza matuka da samun labarin ɗauke ɗaliban.
Ibrahim ya sahida ta bakin Shugaban jami’ar da cewa ɗauke ɗaliban wata barazana ce ga Ilimi a ƙasa, inda ya yi kira da a kuɓutar da ɗaliban.
A sanarwar, Shugaban jami’ar ya jajantawa iyayen ɗaliban, inda ya tabbatar musu da cewa a na ƙoƙarin a ga an kuɓutar da su.
Ya ce tuni dai Shugaban jami’ar ya ziyarci wajen da a ka yi garkuwa da ɗaliban domin ganinsa ido, inda ya ƙara da cewa tuni ya rubuta rahoto ga ƴan sanda domin ɗaukar matakin gaggawa.
Ya kuma yi kira ga ɗaliban makarantar da su kwantar da hankalinsu, su kuma ci gaba da harkokin su a harabar jami’ar.
Da a ka tuntuɓe shi, Ramhan Nansel, Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta jihar, ya tabbatar da cewa hukumar jami’ar ta sanarwar da rundunar abinda ya faru.