Hakimin Kuraye da ke karamar hukumar Charanchi a Jihar Katsina, Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu, ya mayar da martani kan zargin da masarautar Katsina ta yi masa na yin murabus.
Idan za a iya tunawa dai wata sanarwa da masarautar ta fitar ta ce an kwace masa sarautar Sarkin Kurayen Katsina bisa umarnin Gwamnatin Jihar Katsina.
Sai dai kuma a wata sanarwa da daraktan yada labarai na sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Aliyu Yar’adua ya fitar ya ce an tilasta masa yin murabus ne ba bisa shawarar masarautar Katsina ba.
Da yake mayar da martani game da lamarin ta wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Alhaji Ahmadu ya ce, “Ba da son raina na amsa wasiku guda biyu da ke dauke da ranar 18 ga watan Satumba 2023, wadanda suka yi ta yawo a kan cewa na yi murabus daga mukamin Hakimin Kuraye.
“Wasikar farko ta zo ne daga majalisar masarautar Katsina, wadda a bangare guda ta bayyana cewa na yi murabus bisa ga umarnin da gwamnatin jihar ta ba ni.
“Wasika ta biyu ta kasance ne kamar wata sanarwar manema labarai da daraktan yada labarai na gwamnatin jihar ya fitar, inda ta bayyana cewa na yi murabus bisa amincewar shawarar da masarautar Katsina ta ba ni a kan wani laifin da ake zargi na da shi na gudanar da wani daurin aure ba tare da takardar shaidar likita ba, inda ya bayyana daya daga cikin ma’auratan yana dauke da kwayar cutar kanjamau.
“Tare da mutuntawa, gwamnati da majalisar masarautu da alama suna zargin juna, duk da cewa takardar koken ya samu asali ne daga gwamnatin jihar ba masarautar da nake aiki da ita ba a matsayin Hakimi.”
Basaraken da ake zargin ya kara da cewa, hakika mutanen biyu da ake magana a kai (ma’auratan) sun tuntube shi domin ya jagoranci aurensu.
Ya bayyana cewa kamar yadda dokar ta tanada kan nuna kyama ga masu dauke da cutar kanjamau, ya kai su wurin likitan, inda daga bisani kuma ya kai su wurin hukumar yaki da cutar kanjamau ta jihar (SACA).
“An ba su shawarar da ta dace game da wannan auren kuma dukkansu sun amince da su bi ka’idoji suka shimfida.
A irin wannan yanayi sananne ne cewa idan mutum daya ko duka bangarorin biyu suna dauke da kwayar cutar kanjamau, doka ta hana nuna kyama da wariya ga duk wani batun takardar shaida daga likita.
“Dukkanin bayanan da suka shafi wannan lamari, da suka hada da wasikar yarjejeniya daga wurin mutumin, magungunan da likitan ya ba da shawarar, masu ba da shawara na SACA da yarjejeniyar sirri da aka gabatar ga gwamnatin jihar. A bari jama’ar da aka yi wa wannan rashin adalci su zama alkalai,” in ji shi.
Ba a dai bayyana ko an bai wa basaraken damar ba da nasa shaida kafin a yanke hukuncin ya yi murabis ko a’a.
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin, Malam Dikko Umar Radda ta ba da umarnin cire rawanin Sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye a karamar hukumar Charanci bisa zarginsa da daura aure da mai cutar kanjamau.
Bayanin haka yana kunshe ne a cikin wasu takardun guda biya masu karo da juna wanda gwamnatin ta fitar da kuma masarautar Katsina.
Takardar farko da masarautar Katsina ta aike da korar Hakimin wanda sakataren masarautar Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo ya sanya hannu ta bayyana cewa an yi wa sarkin Kurayen Katsina, Alhaji Abubakar Al’adu ritaya ne bisa umarni da masarautar ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari.
“Ta ce bisa umarni da muka samu daga ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Katsina mai lamba KTS/SGS/SEC.54/T/7 ta ranar 15 ga watan Satumbar 2023 a kan maganar daurin auran Alhaji Lawal Mamman Auta da Hajiya Halimatu Abdullahi Kuraye wanda haka tasa gwamnati ta ba da umarnin yi maka ritaya daga mukaminka.”
Sai sanarwar ta ci gaba da cewa bisa wancan umarni na gwamnatin Jihar Katsina masarautar Katsina ta yi wa sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye ritaya daga mukaminsa a ranar Litinin 18 ga Satumbar 2023.
Jim kadan bayan wancan sanarwar ta fadar mai martaba sarkin Katsina, sai kuma ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Katsina ya fitar da wata sanarwar ga manema labarai wanda daraktan yada labarai, Abdullahi Aliyu ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa bisa la’akari da shawarwarin masarautar Katsina gwamnati ta amince da yi wa sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye, Alhaji Abubakar Abdullahi Amadu ritaya daga mukaminsa na hakimi.
Haka kuma sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan wani korafi ne da aka shigar wanda gwamnatin jihar ta amsa a kan tsohon Hakimin wanda kuma aka tura wa masarautar Katsina ta gudanar da bincike kan zargin a kan tsohon Hakimin, sannan ta same shi da laifin yin jagorancin daura aure da mai dauke da cutar kanjamau.
Toni dai masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan wadannan takardu masu karo da juna, inda masautar Katsina ke kokarin wanke kanta daga zargin da cewa umarni ta samu daga sama kafin yi wa hakimin ritaya, a yayin da gwamnatin Jihar Katsina ke cewa masarautar ce ta gudanar da bincike ta kama Hakimin da laifi kafin daukar matakin.
Sai dai kuma wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa korarar hakimin yana tsama da mai garin Kuraye wanda yake baban amini ga gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda wanda dukkan su ‘yan asalin karamar hukumar Charanci ne baki daya.
Source: LEADERSHIPHAUSA