Zaben 2023: Bin diddigin kalaman ƴan takarar shugabancin Najeriya
Yayin da ya rage ‘yan kwanaki a gudanar da babban zaɓen Najeriya, ‘yan takarar da ke son maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari na yin wasu kalamai kan muhimman batutuwan da suka dami kasar.
Mun duba kalaman da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ma mulkin kasar da ‘yan takara biyu daga bangaren hamayya; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour. Peter Obi: ‘Yayin da alkaluman wadanda ke fama da talauci a India kashi 16 cikin 100 ne, na Najeriya kuwa kimanin kashi 63 cikin 100 ne… inda aka saka kasar cikin rukunin kasashen da al’ummarta ke fama da matukar talauci’
Mista Obi ya yi amfani da alkaluma ne daga wurare biyu marasa a alaka da juna.
Alkaluman da ke cewa Indiya na da kashi 16 cikin 100, ya dauko ne daga wani rahoton da aka wallafa a 2022 tare da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kuma cibiyar Oxford Poverty and Human Development Initiative (OPHI).
Sai dai yayin da alkaluman Indiya suka kasance daidai, a cikin wannan rahoton an bayyana alkaluman Najeriya a matsayin kashi 46.4 cikin 100 ne – ba kashi 63 kamar da Mista Obi ya furta ba.
Saboda haka alkaluman da Mista Obi ke magana a kai sun fito ne daga wani rahoton na daban, wanda sahihancinsa na da rauni.
Farfesa Sabina Alkire ta cibiyar Oxford Poverty and Human Development Initiative (OPHI) ta ce yin amfani da alkaluman daga rahotannin da ba su da alaka babban kuskure ne.
Mista Obi ya kuma yi ikirarin cewa “Najeriya ta sha gaban Indiya a matsayin kasar da ta fi samun katutun masu fama da talauci a tsakanin kasashen duniya.”
Sai dai wani mizanin yawan al’ummomin da ke fama da talauci a duniy mai suna World Poverty Clock ya fara bayyana Najeriya ne a gaban Indiya cikin rahotonsu na 2018.
Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam’iyyu suka yi muku
Alkaluma na baya-bayan nan na cewa Najeriya na da mutum mliyan 71 ne da ke fama da matsanancin talauci (wadanda ke rayuwa a kasa da dala 1.90 a kowace rana), idan aka kwatanta da mutum miliyan 44 da ke Indiya. Atiku Abubakar: ‘Cikin shekara biyar, tsakanin 2015 zuwa 2020, yawan wadanda ke da aikin yi ya yi kasa da kashi 54 cikin 100 – daga mutum miliyan 68 zuwa mutum miliyan 31.’
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP mai hamayya da gwamnatin Najeriya, wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasar daga 1999 zuwa 2007, shi ne ya furta haka a watan Janairu.
Bai yi kuskure ba da ya ambato alkaluman masu aikin yi na shekarar 2020.
Sai dai alkaluman da ya furta na 2015 sun hada da wadanda suka bayyana kansu a matsayin ba su da cikakken aikin yi – wanda ke nufin ba sa yin aiki na sa’o’in da ake bukata a kowane yini.
A 2015 kuwa akwai mutum miliyan 55 da ke da cikakken aikin yi, kamar yadda alkaluman gwamnatin kasar suka nuna, abin da ke nufin alkaluma mafiya sahihanci na fadawar da aka samu na yawan masu aikin yi bai zarce kashi 44 cikin 100 ba. Bola Tinubu: ‘Rashin tsaro ya ragu sosai… a baya, muna da tutocin mayakan kungiyoyi masu ikirarin jihadi a Najeriya, a halin yanzu babu wannan al’amarin’
Matsalar tsaro ta kasance babban batu a lokutan zabe, musamman yaki da kungiyoyi masu tayar da kayar baya kamar Boko Haram.
Cikin wata hira da ya yi da BBC ta baya-bayan nan, Mista Tinubu na jam’iyya mai mulki ta APC, ya yi kokarin kare ayyukan samar da tsaro da shugaba mai-ci Muhammadu Buhari ya yi, wanda shi ne jagoran jam’iyyar.
Ya yi ikirari cewa mayakan kungiyoyi masu ikirarin jihadi sun mamaye wasu jihohi hudu na kasar yayin da Buhari ya zama shugaban kasa, inda ya ce a yanzu ba haka lamarin yake ba. “Tuni mun bar matsalar a baya,” in ji shi.
Davida Malet na Jami’ar American University ta birnin Washington DC wanda ya dade yana binciken matsalar da mayakan Boko Haram ke haifarwa tun 2005, ya ce da wuya a iya cewa ga yawansu a Najeriya, sai dai ya ce lallai kasancewarsu a kasar matsala ce babba:
“Ganin cewa kungiyar IS na shigar da mutane cikin kungiyar, lallai akwai mayakan kungiyar a makwabtan kasashe, saboda haka babu mamaki akwai su da yawa a cikin Najeriya ma.”