‘Yan majalisa sun titsiye shugaban ASUU kan zargin cewa Gbajabiamila ya yaudari ƙungiyar
Wasu mambobin majalisar wakilan Najeriya sun titseye shugaban ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke, kan wasu zarge-zarge da ya yi na cewa kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya yaudari ƙungiyar wajen jan hankalinta domin janyewa daga yajin aikin da ta shafe watanni tana yi.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa a wata hira da shugaban ASUU ya yi da wata jarida a ƙasar ranar talata ya zargi Gbajabiamila da cewa ya yi amfani da yaudara wajen sanya ƙungiyar janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana gudanarwa a watan Oktoba.
Ta hanyar rubutaccen alƙawarin cewa gwamnatin tarayya za ta biya malaman duka albashin watannin da ta riƙe musu ba tare da ɓata lokaci ba.
Yayin da yake mayar da martani game da zargin na shugaban ASUU a Abuja, mai magana da yawun majalisar wakilan ƙasar Benjamin Okezie Kalu ya ce babu inda kakakin majalisar ya yi alƙawarin warware matsalar albashin da malaman ke bin gwamnatin tarayya bashi.
Inda ya ce majalisar wakilan ta taimaka ne kawai wajen kawo ƙarshen yajin aikin, ta hanyar yin ƙoƙari wajen inganta albashin malaman jami’o’in tare da taimakawa wajen samar da kuɗin inganta jami’o’in ƙasar.