Hausawa wasu mutane ne masu son girmama al’adunsu da kuma girmama na gaba da su, shi ya sa a ko’ina a kan sami Bahaushe da wuya ya rena na gaba da shi sai dai, ya girmama shi, saboda haka ne ya sa baya ambaton mutum da sunnan yankansa kai tsaye, sai dai ya sami sunan da zai lakaba masa don ya boye wa mutumin sunansa na yanka.
Saboda shi a ganinsa, kiran sunan kai tsaye reni ne. Wannan sunan da aka sanya wa kishiya ranar aurenta yana da mutukar mahimmanci ga al’umar Hausawa, domin mutunci aka sama wa kishiyar yadda yaran gidan ko kannen miji, ba za su kira ta da sunanta na yanka ba, sai dai su kira ta da sunan aure.
Wannan shi ne muhimmancin sunayen da ake sanya wa mata kishiyoyi Hausawa.
Wace ce kishiya a wurin Bahaushe?
kishiya” ta samo asali ne daga ‘kishi’ wanda take nufin rashin jituwa da nuna kyashi irin wanda matan da ke auren mutum daya ke yi wa juna ko kuma nuna gaba a kan wata mace.
Haka kuma Kishiya na nufin abokiyar tarayya a wasu al’amurar rayuwa ta bangaren auratayya, wato, abokiyar zama ko mataimakiyar al’amurar zamantakewar aure.
Ire-iren wasu sunayen kishiyoyi da dalilan samuwarsu
Dangane da ire-iren sunayen da mata suke sanya wa ‘yan uwansu kuwa a lokacin bukin aure da yayin budar kai ya samo asali ne bisa ga dalilai kamar haka:
Lokaci
Zance
Dangantaka
Habaici
Soyayya da sauransu
Ga irin sunayen kamar haka:
Abingani:- Wannan sunan uwargida ce take yi wa Amaryarta habaici, saboda ta fita kyaci.
Don haka sai ta ba ta sunan ‘Abingani’.
A wankesu:- Wannan suna ana rada wa matar da ta fi sauran matan da ke cikin gida kyau. Wannan suna ne da dangin uwar gida ko dangin miji ke samarwa.
Ba-zata: – Wannan suna, uwargida ce take rada wa amarya kasancewar ango bai shaida wa uwargida zai kara aure ba.
Biyayya: – Wannan suna ce da ake rada wa Amarya don ta yi ladabi da biyayya ga mijinta da uwar miji da kuma danginsa.
Bukata:- matar da ake ganin cewa ta shigo gida za ta cike wani gibi wadda sauran matan ba su cika ba.
Dala – Amaryar da aka auro kuma ana zaton cewa ba za ta sami kudin budar kai sosai ba, kuma sai aka sami akasin haka ta sami kudi na fitar hankali, to, a nan sai a kira ta da ‘Dala’.
Dangana: – wacce ba ta son mijin amma an fi karfinta saboda bin maganar iyayenta.
Goshi – Irin wannan suna, suna ne da ake rada wa mace a lokacin aurenta idan har ita matar ko Angon ya yi samu sosai da wadata.
Hana-bege – A nan dangin miji ko uwar Amarya ce take rada wa Amaryar ganin ita ce mace ta hudu a wajen angon. Ma’ana ta rufe kofa babu dammar auren wata mace, kamar yadda addinin Musulunci ya gindaya.
Hakuri:- matar da ake ganin cewa za ta iya hakuri da mijin a sakamakon wata damuwa da ya shiga ciki.
Hana-gori – Mutumin da aka fidda tsamani zai yi aure domin ko zancen auren ma bai yi. A duk lokacin da ya yi aure ana kiran Amaryar da suna ‘Hanagori’. A bin nufi a nan shi ne ba za a yi masa gorin cewa bai taba aure ba.
Hana-kuka – Idan mijin ya nemi aure cikin dangi amma auren bai yiwu ba, sai ya je ya nema cikin bare to, idan aka yi auren sai a kira ta da suna ‘Hana kuka’
Hasada:- matar da lokacin neman aurenta hasada ta yi yawa a cikin neman aurenta.
Ladabi:- Idan aka sami rashin jituwa tsakanin sauran matar da dangin miji to, idan aka auro wata to, sai dangin mijin su sa mata ladabi.
Marka – Wannan suna ‘yan uwan Angon ne ke ko uwargida ke rada wa Amarya dangane da lokacin da aka yi aure. Misali idan da damina ne a lokacin da ake cikin ruwa na marka-marka.
Matar so – Amarya ce da ango ke dokin aurenta, kana yana nuna bambanci a tsakanin sauran matansa na gida, ita ake kira da matar so.
Mowa – matar da take bin uwargida a cikin gida, wato, mata ta biyu a wurin miji ita ake kira da suna ‘Mowa’.
Na-huce – Galibi uwar Angon ne ke rada wa Amarya wannan suna saboda dalilai rin nata ko dai rashin jituwa da uwargida don haka sai ta rada wa Amaryar wannan suna “Na-huce”
Nasara – Mace ce da ta sami masoya da dama masu hannu da shuni amma daga karshe sai wani talaka ya fito, ya aure ta to, wannan ita ake kiranta da suna ‘Nasara’.
Rabo – Rabo suna ne da ake rada wa Amarya saboda wasu dalilai kamar haka; watakila ita budurwar ko Amaryar ta yi manema sosai, har ta kasa fidda gwani cikinsu sai wani daban daga baya cikin manemanta ya zo ya aure ta don haka ake kiranta ‘Rabo’.
Ruwan-jira – Idan iyaye suka kama wa ‘ya’yansu mata ko mazan aure tun suna kanana har zuwa lokacin aure ana kiran Amaryar da ‘Ruwan-jira’.
Saduda – wannan suna ne da ake rada wa Amarya da ta sami uwargidanta mai karfin iko a gidan mijinta. Idan ta auro Amarya sai dangin miji su sa mata suna ‘Saduda’ wato, ta yi hakuri da abin da ta tarar a gidan mijin.
Shalele – Wannan suna ne da ake bai wa yarinyar da ta sami gata a wurin dangin mijinta na ba su ganin laifinta. Don haka bayan ta yi aure sai a ba ta wannan suna ‘shalele’
Sha-yabo – Mace ce da ake zaton cewa in ta shigo gida za ta kyautata wa dangin mijinta.
Shukura – Wannan suna uwar miji ce, ko wasu ‘yan uwan miji ke rada wa amarya. Har illa yau, suna ne da ke nuna godiya ga Allah (SWT).
So-Dangi – Wannan suna ana rada wa mace da ta auri namiji wanda suke da danganta. Ma’ana ‘yan uwan juna ne.
Ta-Annabi – Suna ne da ake bai wa yarinyar da ta girma ba masoyi, ana gudun bacin rana, sai mahaifinta ya hada ta da wani namiji da bai neme ta ba a kan sadaka.
Ta-fisu – Abin nufi a nan shi ne macen da iyayenta suke karamci fiye da iyayen ragowar mata, ko kuma ragowar matan cikin gidan kyau, da natsuwa don haka uwar miji ko dangin miji su sa mata suna ‘Ta-fisu’.
Ta-malama – Ana kiran Amaryar da ta fito, daga gidan malamai da wannan suna.
Ta-sidi – Wannan suna ne da ake bai wa Amarya da ba ta dandana zakin soyayya ba. Irin wannan auren a kan dauke wa Angon kudin sadaki.
Wadata – Wannan suna ne da ake rada wa Amarya wacce a lokacin aurenta gidan miji ya wadata da abin masarufi ko n wasu a abinci ko zaman lafiya.
Wa-ka-raba:- ana sa wannan sunan ne da niyyar cewa wannan auren ya yi karko har iyakacin rai da mutuwa ma’ana wa-ka-raba ban da Allah.
Yawo:- Ana nufin sabuwar Amarya a cikin gida ita ake kira yawo.
Yaya/Yawuro:- Matar dan fari a cikin gida. Wato, suruka matar dan farko na iyaye.
Yelwa:- matar da saurayinta yake cikin matsin rayuwa, amma da ya fara neman ta sai Allah ya yalwata shi da abin hannu.
Zaman-duniya – Wannan suna ne da ake sanyawa Amaryar da ta fi mijinta wayewa ko wace ta fi shi karfi wato na aji ko na arziki ko kuwa kilaki ce.
Zaman-Jira:- ita kuma matar da aka ba wa mijin tun tana karama har Allah ya sa ta yigirma sannan ba ta sauya ra’ayi ba.