A gabatarwan littafin sa wanda shi ne tamkar fitila ga ‘yan kwaminis a shekarar 1848, Marx ya yi iƙirarin cewa; “gabaɗaya tarihi na al’umma, har wacce za ta zo a gaba, tarihi ne dake cike da fafatawa tsakanin ɓangarori biyu”.
Wannan shi ne asasin duk wata fahimta ta Marx. Domin kuwa a baya da yanzu da ma waɗanda za su zo nan gaba, dole za a ci gaba da samun saɓani tsakanin masu ƙarfi da marasa ƙarfi; ƙarfi na arziki, ba ƙarfin damtse ba.
Idan masu mulki ko dukiya suka samar da yanayin rashin yin adalci wurin raba arzikin ƙasa, nan ne za a fara samun karo da juna a tsakanin masu danniyar da waɗanda ake dannewa.
Iya rashin adalci wurin raba arziki ko bayar da haƙƙi ba zai iya haifar da rikici ko saɓani a tsakanin waɗancan ɓangarori biyu ba. Marx ya ce, dole ne sai waɗanda ake zalunta ko dannewa sun yi tarayya wurin fahimtar haƙiƙanin halin da suke ciki, sannan za su fara dasa ayoyin tambaya kan irin rashin mutuncin da ake aikata musu.
Wannan tarayya ta fahimtar halin da suke ciki ne zai sa talakawa ko waɗanda ake zalunta su yi ta haɗa kansu, su yi ta haɗa ƙarfi har su haifar da rikici.
Wani abu mai muhimmanci a wannan tunani na Karl Marx shi ne, su talakawa ko waɗanda ake dannewa idan suka haɗe, suka samar da shugabanci da kyakkyawan tsarin isar da saƙo a tsakaninsu, wannan zai basu ƙarfi. A daidai lokacin da suka cimma wannan mataki, su kuma masu kuɗi ko masu mulki da iko za su yi rauni, su rarraba. Don haka a fahimtarsa, idan aka samu haka, za a samu ɓarkewar rikici. Wannan rikicin shi ne zai haifar da sauyi cikin al’umma bisa turbar adalci.
A taƙaice dai, idan ta ajin Marx za ka bi don fahimtar wannn makarantar ta Conflict, toh yana ƙoƙari ne ya yi bayanin irin saɓani, ƙiyayya, gaba, rashin adalci, da take haƙƙin da ake fama da shi a tsakankanin mutane, wanda waɗannan su ne silar afkuwar duk wani rikici; shi kuma rikicin shi zai kawo sauyi daga wani mataki zuwa wani.
Da yawan mutane ba su sani ba cewa, akwai saɓani tsakanin Karl Marx da wasu masana a wannan makaranta ta Conflict. Misali, George Simmel ya saɓa da Marx a yanayin yadda yake kallon wannan makaranta da kuma bayaninta ga rayuwar al’umma. Simmel bai yarda da batun kasa al’umma gida biyu da Karl Marx ya yi ba; wato tsakanin masu arziki ko mulki da talakawa. A maimakon haka, Simmel ya kalli abin ne ta fuskacin mu’amalar dake tsakaninmu a ɗaiɗaiku.
Simmel yana cewa, ita mu’amala a cikin al’umma akwai wacce ta fi muhimmanci, ita ce tsakanin shugabanni da mutanensu. Tsakanin jagorori da mabiya. Haka nan su kansu waɗanda ake shugabanta ko jogoranta suna da tasu mu’amalar tsakaninsu da iyalai, ‘yan uwa, abokan aiki da sauransu. A nan za mu iya fahimtar cewa, Simmel ya nuna mana akwai matakai na mu’amala kuma a kowacce za a iya samun saɓani a yi rikici.
Ya ce, ita mu’amala ba a raba ta da zaman lafiya, rikici, soyayya da ƙiyayya. Idan ka kalli Nijeriya za ka fahimci wannan. A wasu jihohin ana da zaman lafiya daidai gwargwado, irinsu Kano da Legas. Amma idan ka kalli Zamfara da Maiduguri yaƙi suke fama da shi, inda Jihar Enugu kuma ke fama da kwantaccen rikici. Babban misalin soyayya da ƙiyayya ita ce Jihar Filato. Gabaɗaya zub da jinin da ke faruwa a Filato yana da alaƙa ne da maye gurbin soyayya da ƙiyayya.
Lewis Coser a nashi mahangar, ya tafi kan cewa akan samu rikici mai amfani a cikin al’umma. Kenan a nan Coser ya saɓa da Karl Marx da George Simmel. Coser ya ce, ba zai yiwu a ce rikici ba shi da wani amfani a cikin al’umma ba, saboda yanayi ne dake haifar da canji. Rikici kan sa a samar da sabbin hanyoyin ƙirƙire-ƙirƙire. Rikici musamman a lokacin yaƙi na taimakawa a samar da haɗin kai ta hanyar samar da ƙarfin iko ɗaya.
Misali, a yanzu da Nijeriya ke fuskantar mawuyacin hali na ‘yan bindiga, kusan mafi yawa na mutane an yi tarayya akan addu’o’in samun nasara a kan waɗannan ‘yan bindiga. Irin wannan haɗin kai ɗin da ake samu na baiɗaya a tsakanin mutane yana da amfani, domin duk ƙoƙarin mai mulki ba zai iya samar da shi ba, wani dalili ne kawai ke kawo shi.