Taken Waken Salaam Farmande A Filin Wasan Azadi Na Babban Birnin TehraSalaam Farmande taken waken da ya girgiza duniya kuma sassa daban daban na Al’ummar duniya suka dauka.
A ranar alhamis 26 ga watan may ne babban mawaki dan asalin Jamhuriyar musulunci ta Iran, Abu-Zarr Ruhi ya bayyana a filin wasa na Azadi dake babban birnin Tehran, filin wasan dake cin akalla mutum dubu dari yayi cikar kwari inda da dama basu samu shiga ba saboda cika da filin wasan yayi.
An shirya rera waken ne dai domin jaddada mubaya’a ga Imam Mahdi (A.) da kuma nuna tsantsar biyayya gami da’a ga nizamin Jamhuriyar musulunci ta Iran.
Tun da farko dai babban mawaki Abu-Zarr Ruhi ya zagaya garuruwa kamar Isfahan, Mashhad gami da birnin Qom mai tsarki dama wasu sassa na kasar Iran ciki har da wasu sassa na Tehran kafin a yau alhamis 26 ga watan mayu shirya babbar haduwar ta fiye da mutum dubu dari, haduwar da ta tayar da hankulan wadanda basa dasawa da nizamin Jamhuriyar musulunci ta Iran na duniya.
Yara kanana gami da iyayen su sun bayyana yau a babban filin wasan kuma shima babban mawaki Abu-Zarr Ruhi ya bayyana a inda aka rera waken cikin yanayi mai kyau da kuma ban sha’awa.
Anyi taron an kammala lafiya kowa ya koma gida cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Amma sai dai wannan wake mai matukar farin jini a lokaci guda kuma bai yima wasu mutane dadi ba musamman masu adawa da yunkurin tabbatar da adalchi da jagoran juyin juya halin musulunci na Iran.
Tarukan sauraron taren salam farmande ya zo ya sanya farin ciki a zukatan wasu wasu kuma basu ji dadin yadda baitocin taken suka fito da hakikoki na gaskiya da kuma biyayya ga nizami mai tsarkin na jamhuriyar musulunci ta Iran gami da akidodin jiran bayyanar Imam Mahdi (A).