A ranar bikin sallah ne Solomon Dalung ya ziyarci Kano inda ya gana da Rabiu Musa Kwankwaso Barr Solomon Dalung ya hadu da ‘dan takaran shugaban kasan NNPP, ya ce ya ji dadin zaman na su Bidiyo ya nuna Rabiu Musa Kwankwaso ya na yi ‘Dan siyasar rakiya, yayin da za a maida shi masauki.
A ranar Asabar, 9 ga watan Yuli 2022, mu ka samu labari cewa Barr Solomon Dalung ya kai wa Rabiu Musa Kwankwaso ziyara. Daya daga cikin Hadiman tsohon gwamnan na jihar Kano, Saifullahi Hassan ya wallafa hotunan Dalung da Kwankwaso bayan zamansu.
A Wurin Sallar Idi, Ya Ce Shine Dan Takara Mafi Cancanta a 2023 Dalung ya yi farin ciki A bidiyon an ga Dalung yana fadawa ‘dan takarar shugaban kasar na zaben 2023 yana cewa ya yi farin ciki sosai da ya ziyarce shi da bikin idi.
Dalung ya roki Ubangiji ya kara dankon zumunci da hada kan al’umma a zabe mai zuwa, sannan ya yi addu’a ga shugabanni da ke shirin barin mulki.
Tsohon Minista ya canza layi Idan za a tuna, Dalung ya rike Ministan wasanni da matasa a wa’adin farko na gwamnatin Muhammadu Buhari tsakanin 2015 da 2019.
Tsohon ‘dan takaran Gwamnan ya rasa kujerarsa ne bayan APC ta zarce a kan karagar mulki.
Tun bayan nan a kan ji ‘dan siyasar yana maganganun da yake cewa yana fadawa gwamnati gaskiya, wasu za su ga yana kushe ta ne.
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Barr. Dalung ya shirya ne musamman domin ya gana da Kwankwaso a gidan na sa da ke Garin Kano.
Dalung ya shiga NNPP? Mu na da rahoto da Kwankwaso ya kafa tafiyar The National Movement a lokacin da yake shirin ficewa daga PDP, Dalung ya samu halartar taron.
Amma duk da haka, daga baya sai aka ji tsohon Ministan tarayyan ya fito yana nesanta kan sa daga jam’iyyar NNPP da TNM ta narke a ciki.
Abin da ba a sani ba shi ne yanzu ‘dan siyasar ya shiga NNPP ko bai shiga ba, domin an ga shi da jar hula wanda tambari ce a Kwankwasiyya.