Wannan Rana Tana Daya Daga Ranekun Da Aka Ruyawaito Shahadar Sayyidah Fatimah As Kasancewar Matsalar Rubutu Da Aka Samu Wajen Rubuta Ranar Da Tayi Shahada Daga Ciki Akwai Wannan Rana Kamar Yadda Ruwayar Kwanaki 95 Ta Nuna.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti – Abna ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan zagayowar ranar shahadar Sayyida Zahra (a.s), ya kawo maku takaitaccen bayani dangaen da wannan munasabar: Sayyida Zahra (As) ta kasance mai ilimi da mafi girman koyarwar mafi girma tun tana karama a karkashin jagorancin mahaifinta Manzon Allah (SAW).
Ya kasance daya daga cikin abubuwan da Allah ya yi mata, amfana da yawa da tayi daga tushen ilimomin Ubangiji.
Sayyida Zahra (AS) diyar Manzon Allah ce, matar Imam Ali As kuma Mahaifiya ga Imamai da Imamanci, kuma ita ce ta zamo mahada tsakanin Annabci da Imamanci. A tsawon rayuwarta Sayyidah Fatima Zahra (AS) ta kasance mai karamci, sadaukarwa, gafara, hakuri, gamsuwa, bautar Allah da taimakon talakawa ta hanya mafi kyawu,kuma ta tarbiyyanci Mutane masu Girma a tsawon Tarihi Kamar su Imam Hasan da Imam Husaini (as) sun samu tarbiya daga gareta sun tashi a hannunta. Sayyidah Fatimah As, bayan mahaifinta mai daraja, ita ce mutum na farko da ya fara haduwa da Mazon Allah SAWA daga gidan Bani Hashem. Sayyida Zahra (AS) a lokacin shahadarta tana da shekaru goma sha takwas kuma ta haifi ‘ya’ya hudu Imam Hassan da Imam Husaini (a.s) da Zainab da Ummu Kulthum (a.s).
Domin Karuwa Sosai Da Wannan Munasa Mun Tsakuro Maku Kadan Daga Cikin Hudubobin Sallar Juma’a Na Wannan Mako A Alishahr, Ranar 16 Ga Watan Disamba 1402, Da Hujjatul Islam Hamidinejad Limamin Juma’a Na Alishahr
A lokacin ranekun tunawa da Shahadar Sayyida Fatima As wajibi ne a yi nazari tattare ga dalilin shahadarta da kuma kokarin ganin ta zama abin koyi a gare mu, yayin da ya zamo Imamuz Zaman A’a yana cewa. “‘Yar Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, abar koyi ce a gare ni” yayin da kuma Allah Ta’ala yake cewa a cikin suratul Ahzab, Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam “abin koyi ne mai kyau a gare ku to ya tabbata a fili yake cewa Sayyidah Fatima As kamar Annabi ce a wajabcin yin biyayya garemu.
Ayyukan da Sayyida Zahra (a.s) ta yi wanda suke gava da dukkan dukkan ayyukan da ta gabatar, wanda Wannan aikin da ta yi ya sanya aka karya mata hakarkarinta, yayi sanadiyar marinta da a kayi da yi mata wulakanci, daga karshe kuma ya kai ga yin shahada, wannan aikin ba komai bane face kare Imamin Zamaninta da waliyyarsa wand hakan yana daga cikin mafi wajibcin ayyuka a cikinsu.
Bisa dogaro da yadda ayoyin Alqur’ani da suka yi nuni da wajibcin biyayya ga -Ulil Amri-, shin mun yi tunanin dalilin da ya sa Zahra ta zo bayan kofa alhali Ali (a.s) yana cikin gida, tare da cewa Sayyadi Ali (a.s.) ) da Sayyida Zahra dukkansu sun san abin da mutanen da ke bayan kofa su ke da burin aikatawa, kuma da me zai faru idan Sayyida Zahra (a.s) ba ta zo ba, rashin zuwanta wato zai nuna ba ta cika wani muhimmin aiki na addini ba, wato kare imamanci da wilaya kuma da bata aikata hakan ba (Waizubillahi) za tai mutu mutuwar jahiliyyah.
Bisa dogaro da yadda ya zo a hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa wanda Malaman shi’a da Ahlus-Sunnah suka tabbatar da ingancin sa, kamar yadda yazo a hadisai da dama dake tabbatar da wannan lamari gasu kamar haka:
عن رسولُ اللَّهِ صلى اللَّه عليه وآله : مَن ماتَ وَهُوَ لا يَعرفُ إمامَهُ ماتَ مِيتةً جاهليّةً.
وعنه صلى اللَّه عليه وآله : مَن ماتَ ولا بَيْعَةَ عَلَيْهِ ماتَ مِيتةً جاهليّةً .
وعنه صلى اللَّه عليه وآله : مَن ماتَ بغيرِ إمامٍ ماتَ مِيتةً جاهليّةً .
الإمامُ الصّادقُ عليه السلام : مَن باتَ ليلةً لا يَعرِفُ فيها إمامَ زمانِهِ ماتَ مِيتةً جاهليّةً.
Sayyida Zahra (A.S) ta gudanar da ayyukan da suka hau kanta a matakai da dama wajen kare Imamin zamaninta don cika hujja a kan mutane baki daya har zuwa tashin kiyama.
Akwai Matakai guda biyar zuwa shida da Sayyidah Zahra’a A’s ta bi wajen kare Imamin Zamaninta Da Wilayarsa ga su kamar haka:
1- Matakin farko na kasancewarta a bayan kofa.
2- Mataki na biyu shi ne halartar masallaci da gabatar da hudubar Fadak da rokon jama’a da su taimaka wa Imamin Zamanin Su Wato Imam Ali(a.s).
4- Mataki na uku shi ne take gidajen Ansar har darare 40 tana mai nemi taimako daya bayan dayansu domin su taimakawa Ali As Amma ba su amsa ba.
4- Mataki na hudu shi ne na yin kuka, kuka mai raɗaɗi na tsawon awa 24 a dukkan sauran rayuwarta. Wanda ya kamata ace kowa ya tambayi kansa dalilin wannan kuka mai tsanani.
Tun bayan wafatin Ma’aikin Allah SAWa Sayyada Fatimah As ta kasance tana yin kukan rashin maahaifinta manzon Rahama Sawa wanda har takai makotanta sunayin kuka duk lokacin da take yin kuka hakan abun ya zama kamar sarka idan tayi kuka mokatan acikin gidansu daya bayan daya suna amsa wannan kukan nata har wasu lokutan madina ta dauka da kuka gaba daya saboda Manzon rahama bai dade da wafati ba SAWA hakan yasanya mutane suka zo wajejn Imam suka kace Ali kayi wani abu da zai sanya Zahra tadan rage kukanta domin duk lokacin da tai kuka madina tana amsawa ne to Imam Ali Haka ya fadawa Sayyidah korafin mutanen Madina sai tace dashi ya samu wani waje a wajen madina ya kebance mata domin inason dani da yayana inje wajen gari inyi makokin mahaifina inyi kuka saboda rashin shi saboda banso insa ran mutane ya baci akan haka, haka kuwa akai Imam Ali As ya gina mata waje wanda shike kira da baitul Huzni takan je ta zauna tare da ‘yayanta suyi ta kuka. Wanda tun bayan wafatin mahaifinta fuskarta arufe take tana yin kuka tana kara damuwa da ramewa rana bayan rana har lokacin Shahadarta As.
5- Mataki na biyar na sadaukar da rayuwarta ta hanyar yin shahada, watakila ta hanyar hakan mutane za su tashi su taimaki Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi).
6- Mataki na shida shine wasiyya da ta bari ga al’umman da za su biyo baya inda ta bayarda wasiya ga Imam Ali As da cewa yayi mata wanka da dare ya kuka binneta da dare yadda ba wanda zai san inda kabarinta ya ke. Domin gaskiya ta tabbata tare da bayyana a gare su ta yadda wata rana za su zo da tsararraki da za su taimaka wa Imamin zamaninsu.
ثمّ قالت ( عليها السلام ) : ( يا بن العمّ ، إذا قضيت نحبي فاغسلني ولا تكشف عنّي ، فإنّي طاهرة مطهّرة ، وحنّطني بفاضل حنوط أبي رسول الله ( صلى الله عليه وآله ) ، وصَلِّ عليَّ ، وليصلِّ معك الأَدنى فالأَدنى من أهل بيتي ، وادفني ليلاً لا نهاراً ، وسرّاً لا جهاراً ، وعفَّ موضع قبري ، ولا تشهد جنازتي أحداً ممّن ظلمني .
Wanda yanzu akwai aiki babba da ya hau kan kowane musulmi mai amsa sunan musulunci da tunkaho da shi ya bincika tare da gano hakikanin inda kabarinta ya ke domin da sanin hakan zai gane ina gaskiya ta ke kuma me ya hau kansa tun kafin ya koma ga Ubangiji Allah Ta’ala da zai tambaye kuwa kan yadda yayi biyayyawa Annabi Annabawa Muhammad Sawa da yadda yayi biyayya ga wadanda Annabi Muhammad Sawa ya ce abin bayansa wanda hakan kawai shi zai kubutar da mutum a gobe kiyama ranar da Allah Ta’ala zayyi hukunci ga dukkan wanda aka zalunta wanda hukunci farko da za’a fara gudanarwa a gobe kiyama shine ƙarar da Sayyidah Fatimatuz Zahra’a A’s za ta shigar na abi mata hakkinta akan kisan danta Imamul Husaini A’s.
A yau ma Sayyidina Zahra s.a.w tana zuwa kowane a gida kamar yadda ta yita zuwa gidajen mutanen Madina tana cewa su taimakawa sayyida Ali, to a wannan zamanin ma haka ne tama zuwa ta riko al’umma akan su taimakawa Imamuz Zaman A’a tana mai nusatar da mu wane limaminmu na yau, shin muna amsa wannan bukata ta kuwa?
Source: