Sauya fasalin naira: Me zai faru bayan wa’adin da CBN ya bayar ya cika?
Bayan wa’adin da CBN ya saka na 31 ga watan Janairun sabuwar 2023 ya ƙare mutane ba za su iya amfani da tsofaffin takardun naira da aka sauya ba.
A bayanan da bankin ya bayar ya ce dukkanin bankunan da ke da waɗannan takardun kuɗi a yanzu suna iya fara mayar da su CBN ba tare da ɓata wani lokaci ba.
Gwamnan bankin ya ce duk bankin da ya fara kaiwa shi za a fara bai wa sabbin takardun.
Ya shawarci jama’a masu mu’amulla da bankuna waɗanda suke da kuɗaɗen a hannunsu da su fara kai wa asusun ajiyarsu a bankunan domin a samu damar sauya su da wuri.
Sakamakon matakin, ana sa ran dukkanin bankuna su bar cibiyoyinsu na tattara kuɗaɗe a bude daga Litinin zuwa Asabar saboda bai wa ‘yan ƙasa damar mayar da kuɗaɗen a kan lokaci.
Domin hanzarta sauyin, Babban Bankin Najeriya ya dakatar da cajin kuɗin da ake biya na ajiye kuɗaɗe a bankuna wato deposit charge a turance.
Karanta cikakken labarin a nan: Ya za a yi da tsoffin kuɗin da za a sauya a Najeriya?
Read More :
Martanin da hukumomin Falasdinawa suka yi kan shahadar wani matashin Bafalasdine.