Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar II, ya bayyana cewa akalla litattafai miliyan 3.2 daga ayyukan Malaman Addinin Musulunci 200 na Daular Usmaniyya ne aka gyara tare da buga su don rarraba su a fadin kasar nan.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro na kwanaki uku kan koyar da Addinin Musulunci a Afirka wanda ya gudana a dakin taro na Arewa House da ke Jihar Kaduna a ranar Talata.
Taron ya samu hadin gwiwar kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) da cibiyar bincike kan al’adun Musulunci da tarihin Musulunci (IRCICA) Turkiyya da kuma Al Istikama suka shirya.
Sultan Abubakar, ya ce an buga littattafan a cikin harsunan Ingilishi da Larabci da Hausa.
Ya bayyana cewa, baje kolin kayayyakin tarihi na Afirka zai taimaka wajen dawo da martabar ‘yan Afirka da kimarsu a nan gaba.
“Shugabannin Halifanci kadai sun yi rubuce-rubuce sama da 300 kan ayyukan diyar Shehu Usman Danfodio, Nana Asma’u da wasu dalibansa irin su AbdulKadir zul Mustapha.
Wadannan ayyuka sun shafi batutuwa da dama daga sanannun masana kimiyyar Musulunci na tafsirin Alkur’ani, ilimin zamantakewa, tattalin arziki, kimiyyar siyasa da likitanci.
“Ya zuwa yanzu mun gyara tare da buga littattafai sama da miliyan 3.2 na ayyuka 200 na wadannan manyan shugabanni kuma sun zagaya kasa da dakunan karatu na daidaikun mutane da makarantu a fadin duniya.
“Wadannan littafai an buga su cikin harshen Turanci da Larabci da Hausa ne kuma insha Allahu a karshen wannan taro zan kawo wasu daga cikin wadannan littattafai.
Muna cikin zamanin da turawan mulkin mallaka suka boye wadannan ayyuka ta hanyar kin sanya su cikin tsarin karatun makarantun gwamnati don wasu manufofi nasu
“Amma mun kudiri aniyar fito da wadannan ayyuka na ilimi don sanya su cikin harsunan da za su ba da damar yin amfani da su.
Ya kuma kamata taron ya taimaka wajen gano abubuwan da muka gada don ganin sun shiga duniya.”
Shugaban taron, Farfesan tarihi kuma tsohon mataimakin shugaban Jami’ar Jihar Adamawa, Farfesa Al Kasum Abba ya ce babu wani abu da ya wuce tallafin karatu domin babu wata kungiya da za a iya tafiyar da ita bisa jahilci.
“Abin farin ciki ne cewa wannan taro yana gudana ne kan ilimin Musulunci da karatu a Afirka.
Mutane ba su gane cewa tun kafin Turanci ya zo akwai ilimi a Musulunci. Idan aka nutsa cikin tarihi, ilimin Musulunci a Afirka yana da matukar muhimmanci.
“Jihadin Sakkwato wani yunkuri ne na zamantakewa amma Turawan Ingila sun zo suka kira shi da jihadin Fulani saboda suna son kafa tasu daular.
Ba ma yin karatu ba, amma muna tsara guraben karatu na Musulunci yadda ya kamata a tsara shi.
Sarkin Musulmi da Shehun Borno ya kamata su taimaka wajen samar da kudade don nazarin jihadin karni na 19 domin ya dauki matakai daban-daban na jihadin Sakkwato da Borno.
Haka kuma muna bukatar kudi don fassara duk rubuce-rubucen karni na 19 domin mu fahimci tarihin al’ummarmu.”
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, wanda shi ne babban mai masaukin baki, ya ce taron ya zoa kan gaba kuma ya dace wajen bayyana irin gudunmawar da al’ummar Musulmi ke bayarwa ga ilimin duniya.
Gwamnan ya yi nuni da cewa, Daular Sakkwato na kan gaba wajen bayar da gudunmawar ilimi a Afrika.
Ya ce Sheikh Usman Bin Fodio da dan uwansa Sheikh Abdullahi Fodio sun bayar da gudunmawa a fannonin jagoranci na dabi’a, ilimi, noma da kasuwanci.
Sani ya bayyana fatan taron zai samar da wani tsari na sake farfado da ilimin Addinin Musulunci domin ya dace da yanayin duniya wajen bai wa matasa dabarun rayuwa, tare da jaddada cewa yana da kyau a samar wa matasa sana’o’in da za su ba su damar yin takara a duniya da kuma bayar da gudunmawa mai ma’ana ga al’umma.
Taron dai ya samu halartar malaman Addinin Musulunci da masu bincike da masana daga sassa daban-daban na Afirka da ma duniya baki daya.
Daga cikin manyan baki sun hada da Shehun Borno, Alhaji Umar Garbai el-Kanemi, mataimakin gwamnan Jihar Kano, Alhaji Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sauran sun hada da Dokta Usman Bugaje, babban daraktan IRCICA, Mahmud Erol Kilic, babban sakataren kungiyar OIC, Hissein Brahim Taha ya samu wakilcin daraktan kula da harkokin al’adu, mataimakin shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya samu wakilcin mataimakin shugaban hukumar, Farfesa Ibrahim Dogo.