An samu firgici a yau Alhamis 25 ga watan Agusta a unguwar Ijanikin ta jihar Legas yayin da wasu tsageru suka farmaki fadar Oloto na masarautar Oto Awori, Oba Aina Kuyamiku.
Rahoton jaridar Punch ya ce, tsagerun sun lalata motocin basaraken, haka nan sun kone wasu shaguna da ke zagayen yankin.
Yadda ‘yan daba suka mamaye gidan basarake a Legas Baasaraken gargaiya a Legas ya tsere dakyar yayin da ‘yan daba suka mamaye fadar sa.
A wani labarin na daban zunzurutun basin da ake bin Najeriya a halin yanzu ya zarce kudin shigar da kasar ke samu kamar yadda Ofishin Kula da Basussuka ya bayyana.
Darakta Janar ta Ofishin DMO, Patience Oniha, tace yawan kudaden da ake biyan basi ya tasi har ya kai 109% Daga watan Disamban shekarar da ta gabata zuwa Maris na wannan shekarar, Najeriya ta biya N3.83 tiriliyan na bashi.
Najeriya ta kashe kudade masu yawa wurin biyan bashi fiye da wanda take samu tsakanin watan Janairu zuwa Afirilu na wannan shekarar inda darakta janar na Ofishin Kula da Basusska, Patience Oniha.
Yawan kudin da ake amfani da shi wurin biyan bashi ya zama abun damuwa ga gwamnatin tarayya saboda a watanni hudu na farkon shekarar nan ta biya bashi da sama da kudin shigar da take samu.
Darakta janar din ta kara da cewa, yawan kudaden da ake biyan bashi ya karu da kashi 109 tsakanin watan Disamban shekarar da ta gabata da na Maris din wannan shekarar, daga N429 biliyan da N896 biliyan.
DMO Nigeria DMO: Zunzurutun Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Zarta Kudin Shiga da Take Samu.
The Nation ta rahoto cewa, kamar yadda bayanan da ofishin kula da basukan suka bayyana, an kashe N3.83 tiriliyan wurin biyan bashi a kasar nan cikin watanni 15.
Oniha ta sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya cewa, “yawan aron da ake yi ana hada shi da tsarikan aron kudi.
“Duk da a bayyane yake, daya daga cikin abubuwan da kwarraru ke cirewa cikin kiyasin shine sabon salon rancen na nufin karin yawan bashin da kuma bashin da za a biya nan gaba,” tace yayin da take bayyana cewa, Najeriya na bukatar karin kudin shiga da kula da basukan da ake bin ta yadda ya dace.
Source: LEGITHAUSA