Sarkin Daura, Alhaji Dr Umar Faruk mai shekaru 91 ya kara yin wuff da budurwa danya shakaf mai shekaru 22 Kamar yadda aka tattaro, an daura auren ne ba tare da wasu manyan shagulgula ba a makon da ya gabata Tuni dai amarya Aisha Gona Safana ta tare a dakinta inda ta tabbata sabuwar gimbiya kuma amaryar tsohon basarake.
Zukekiyar amaryar mai suna Aisha Gona Safana ta tabbata sabuwar gimbiya a Daura.
A shekara 90, Sarkin Daura ya auri tsaleliyar Amarya ‘yar shekara 20 A wani labari na daban, Daily Nigerian na ruwaito.
Mai Martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya yi sabuwar Amarya, Aisha Iro Maikano, a ranar Asabar.
An tattaro cewa an yi daurin auren bayan dan gajeren lokaci da Sarkin ya hadu da yarinyar wacce diya ce ga Fagacin Katsina, Iro Maikano. Hakazalika rahoton ya nuna cewa an daura auren bisa kudin sadaki N1million.
A wani labarin na daban takaddama ta kaure yau Laraba a Majalisar Dattawan Najeriya lokacin da aka bukaci tattauna matsalar tsaron da ta addabi kasar da kuma bukatar tsige shugaban kasar Muhammadu Buhaari saboda abin da ‘yan majalisun suka kira gazawar sa wajen kare rayukan ‘yan kasar.
Rahotanni sun ce shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal yaki amincewa da bukatar tattauna tsige shugaban kasar, sai dai mahawara akan yadda matsalar tayi kamari da kuma baiwa shugaban kasar wa’adi domin shawo kan su, idan kuma ya gaza sai akai ga bukatar tsige shi.
Bayanai sun ce hana tattauna bukatar tsige shugaban kasar da Lawal yayi ta sanya wasu ‘yan majalisar sama da 10 haure takalaman su domin ficewa daga zauren majalisar.
Kamar yadda rahotanni ke cewa, yunkurin janyo hankalin shugaban majalisar da shugaban marasa rinjaye Sanata Philip Aduda yayi, bayan sun kwashe sa’oi 2 suna tafka mahawara a asirce, yaci tura.
Yan Najeriya daga kowanne bangare sun fusata dangane da halin da kasar ke ciki saboda tabarbarewar tsaro, abinda ya kaiga salwantar da daruruwan rayuka da kuma asarar dukiyoyi.
Ko a makon jiya ‘yan bindigar da suke garkuwa da mutane sun yi barazanar sace shugaban kasar Muhammadu Buhari da Gwamnan Kaduna Nasir El Rufai bayan sun fitar da faifan bidiyo inda suke lakadawa fasinjojin jirgin da suka kama duka.
A wannan mako, Yan bindigar sun kashe sojoji guda 3 a Abuja, babban birnin kasar da kuma kai hari kusa da kwalejin gwamnati dake Kwali, abinda ya tilasta rufe makarantar.
Bayan ficewar ‘yan adawar, majalisar ta baiwa shugaba Buhari wa’adin makonni shida da ya magance matsalar tsaron, ko kuma ya fuskanci tsigewar.
Source:rFi
Source:legithausang