Maimartaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya isa Kano domin karbar takardar nadinsa a karo na biyu daga Gwamna Abba Kabir Yusuf. Bikin wanda aka shirya gudanarwa da misalin karfe 10 na safe a gidan gwamnati, zai hada da jawabai daga gwamna da mai martaba sarki, sai kuma sanarwar mubaya’a daga Hakimai da masu rike da sarautar gargajiya.
A safiyar ranar Alhamis ne aka samu rahoton dawo da Sanusi II, kuma an sa ran zuwansa Kano a safiyar Juma’a. Taron gabatarwar zai kunshi manyan jami’an gwamnatin jihar da sarakunan gargajiya.
A kwanakin baya ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da gyaran kudurin dokar majalisar masarautun Kano ta shekarar 2024 da aka yi wa kwaskwarima, wadda gwamnan ya sanya wa hannu. Hakan ya mayar da masarautar Kano matsayinta na da tun kafin shekarar 2019 tare da rusa sabbin masarautun Gaya da Rano da Karaye da Bichi guda hudu, wanda ya kai ga dawo da Sarki Sanusi II.
DUBA NAN: Kotu A Kano Ta Dakatar Da Ganduje Daga Shugaban Jam’iyyar APC
Taron dai ya gudana ne duk da umarnin wucin gadi da wata babbar kotun tarayya ta bayar na umarnin a tabbatar da zaman lafiya a jira ta yanke hukunci ranar 3 ga watan Yuni mai kamawa, wanda ya nuna irin sarkakiyar da ke tattare da batun dawo da Sanusi II.
A wani labarin na daban shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya tabbatar da cewa, gwamnoni arewa maso gabas sun dukufa wajen ganin sun shawo kan matsalar rashin wutar lantarki da ta ki ci ta ki jinyewa a yankin, a musamman a ‘yan kwanakin nan.
Inuwa ya shaida haka ne ga manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce, rarraba duk wani abu da ya shafi wutar lantarki ya kasance ne cikin jerin kebabbun hakkoki na gwamnatin tarayya, amma yanzu tun da an samar da sabuwar dokar wutar lantarki, jihohi na iya samarwa da rarrabawa.
Gwamnan ya kara da cewa, “Ko a taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas na karshen nan da muka kammala kwanan nan, mun yanke shawarar cewa kowannenmu ya samar da Megawatts 10 na wutar lantarki daga hasken rana, kuma dukkaninmu muna da damar yin aiki da sabuwar dokar samar da wutar lantarkin, mun san cewa daga yanzu dogaro kan kaifi daya kawai ba zai kai mu ba. Duk abin da muke da shi bai iya fitar da mu daga wannan hali ba”.