An yi gagarumar liyafar cin abincin dare ta kammala shagalin rakashewar auren Yacine Sheriff da Shehu Yaradua a Abuja inda ‘yan uwa da abokan arziki suka dinga tururuwar zuwa.
Manyan mata a kasar nan da suka hada da Aisha Buhari, Patience Jonathan da kuma Turai Yar’adua, mahaifiyar angon sun samu halarta.
‘Ya’yan manyan kasar nan da suka hada da Zarah Bala Muhammad, Malah Sheriff, Mahmud Mamman Legas, da sauransu sun haskaka wurin da salon rawansu.
Amarya da angonta ba a bar su a baya ba, bayan iyaye sun kammala abinda zasu yi, sun kama gabansu, sun sauya kaya inda suka girgije cike da murna.
A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli 2022 ne aka yi kasaitacciya kuma gagarumar liyafar cin abincin dare ta kammala shagalin rakashewar auren Shehu Yaradua da amaryarsa Yacine Sheriff.
Duk da an daura auren tun ranar 23 ga watan Yulin 2022, bayan nan an sake balle sabon shagalin bikin wanda ya dinga samun halartar manyan baki a kasar nan.
Bidiyoyi da hotunan raƙashewar ‘ya’yan manyan kasar nan a liyafar Yacine da Yaradua, Aisha Buhari ta halarta.
Ba Aisha Buhari kadai cikin matan manyan kasar nan ta samu halartar liyafar ba, uwargidan tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, Patience Jonathan ta samu zuwa wurin.
An bai wa Aisha Muhammadu Buhari damar yin jawabi kafin ma’auratan sun yanka kek din auren nasu.
Daga cikin ‘ya’yan manyan kasan nan da suka girgije tare da rakashewa a wurin liyafar akwai, Mahmud Mamman Legas, Malah Sheriff, Zarah Bala Muhammad da sauransu.
A wani labari na daban, ‘dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar’adua, Shehu Yar’adua ya yi wuff da Yacine Muhammad Sheriff a Maiduguri dake jihar Borno a yau Asabar, 23 ga watan Yulin 2022.
An daura auren a gidan Sheriff wanda yake kusa da barikin Giwa kuma ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilci daga ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, Gwamna Babagana Umara Zulum da takwarorinsa na jihar Kebbi da Jigawa.
Kawun amarya kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ya jagoranci wasu jiga-jigai da suka hada da tsohon gwamnan jihar Niger.
Adamu Mu’azu, tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje, tsohon gwamnan Kastina, Ibrahim Shema, tsohon gwamnan Kebbi, Adamu Aleiro, tsohon gwamnan Bauchi Isa Yuguda, tsohon SGF Yayale Ahmed, tsohon gwamnan Zamfara Ahmed Sani Yarima da kuma shugaban NNPC Mele Kyari da sauransu.
Source:hausalegitng