An watsa rubutun Shahid Murtaza Mutaharri wanda ba a fitar ba a shekarata 1342 a cikin gidan yari
Bayan jawabin Imam Khumaini na ranar 13 Khurdad 1342, An Kama Imam da kansa da Ayatullah Sayyid Hassan Qumi da Baha’uddin Mahalati, da wasu malamai 11 da suka hada da Ayatullah Muhammad Taqi Filasfi, Murtaza Mutaharri, Abdul Husain Dastghib da Nasser Makarem Shirazi, inda aka kama su na dan lokaci an kai su gidan yarin na wucin gadi na birnin Tehran Shi ma Hujjatul-Islam Islam Muhsin Muhaddiszadeh Qumi dan marigayi Sheikh Abbas Qummi yana daya daga cikin wadanda ake tsare da su, kuma a lokacin ya bukaci mutanen da ke wurin da su rubuta masa dan tsokaci a cikin littafinsa na rubutu dake tare da shi.
Da Sunan Allah Mai Girma Da Daukaka
الذین یستمعون القول فیتّبعون احسنه، اولئک الذین هدیهمالله و اولئک هم اولواالالباب.
Kamar yadda idan mutum ya yi tafiya a kan titi da kasuwa, ya kan lura da abubuwa daban-daban kuma sha’awar saye ta taso a gareshi, kuma dole ne shi da kansa ya kasance yana da ikon ganewa da siyan abubuwa masu kyau da dacewa da kansa, haka abun yake a bangaren tunani da ilimi da ruhi su ya kamata mutum ya zabi abin da ya dace.
Ya kasance yana jin bayanai daban-daban a cikin kunnuwansa kuma yana ganin rubuce-rubuce daban-daban da idanunsa, kuma dole ne shi da kansa ya kasance yana da ikon ganewa da suka akan abubuwa, kuma dole ne ya zama abinda yake ji da gane na magana ya iya bambanta daidai da mai kyau da wanda ba daidai ba da mara kyau, haka ma ya yi la’akari da halin da yake ciki, wajen zabama kansa abunda ya dace da shi, kuma ya zabi gwargwadon halin da yake ciki, in ba haka ba sai y zamo ya barnatar da dukiyarsa ta ruhi da ilimi, ya lalata rayuwarsa.
Ya kamata mutum ya san cewa na farko, duk wata magana da ya ji daga bakin wani, ko da kuwa wannan babban mutum ne, ko abin da ya gani a littafi, ko da mawallafin wannan littafi babban mutum ne, ya dauka ba gaskiya ba ne, na biyu kuma ba duk maganar gaskiya ce ba take da amfani ga kowa.
Karkashin ayar Karima dake cewa:
فلینظر الانسان الی طعامه
Bisa tafsirin da akai mata kowa ya kiyaye cikin abincinsa na ruhi ya sanya hankali kada ya shigo da kowane irin tunani cikin ruhinsa.
Ali Alaihi salam yana cewa:
ما لِی أرَى الناسَ إذا قُرّبَ إلیهمُ الطعامُ لیلاً تَکَلّفُوا إنارةَ المصابیح…
Ya zo a cikin ruwayoyinmu cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam ya ce ku koyi hikima a duk inda kuka ganta kuma a hannun kowa ko da kuwa shi kafiri ne ko mushriki.
کونوا نقّادالکلام…
Sai dai daya daga cikin baiwar Allah ita ce mutum yana da ikon yin suka, da yin hukunci da iya magana, da rashin bata lokacinsa kan al’amura marasa amfani, don yin amfani da basirarsa. kamar yadsa Ayar Kur’ani take cewa:
الذین یستمعون القول فیتبعون احسنه
tana tunatar da mu da wannan ma’ana. A cikin wannan ayar, an yi amfani da kalmar “استماع”, wato tana nufin ‘saurare’, ba kalmar ‘سماع’ ba, dake da ma’ana ‘ji’ ba kuma a qarshen ayar madaukakiya tana ganin masu hikima ne kawai suke iya anfana da wannan. Domin a fili yake cewa idan har karfin hankali bai ci gaba ba kuma bai kai matakin balaga ba, ba zai yiwu a zama mai iya tantancewa ba tsakanin mal kyau da marar kyau balle har yayi hukunci akai.
Wadannan ‘yan kalmomi ne a gidan yarin Shahrbani na wucin gadi na birnin Tehran a ranar 13 ga watan Safar shekara ta 1383, wato rana 31 da zamanmu a wannan wuri, kuma a wannan lokaci na yi farin ciki da haduwa da gungun manyan malamai da masu wa’azi a matsayin abin tunawa da ke cikin littafin Hazrat Mustatab Siqatul Islam Makhdoomzadeh, Mai girma Malam Haj Mirza Momuhsen Muhadis zadeh Qummi dana samu rubutawa.
اللهم انّا نَرغَب الیک فی دوله کریمه تعز بها الاسلام و اهله و تذل بها النفاق و اهله و تجعلنا فیها من الدعاه الی طاعتک و القاده الی سبیلک و ترزقنا بها کرامه الدنیا و الآخره.