Ministan Wutar Lantarki ya ɗau nauyin marayu 16 a makarantar kwana ta kuɗi a Yobe
Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, ya ɗauki nauyin yara marayu 16 su yi karatu a makarantar kwana ta kuɗi, mai suna El-Kanemi College of Islamic Theology Maiduguri.
Tun da farko, marayun sun kammala zaman su na gidan marayu da ministan, wanda ya buɗe, mai suna Ya Zarah Orphan Care Foundation, a Potiskum a Jihar Yobe domin yaran da su ka rasa iyayen su sakamakon yaƙin Boko Haram a Arewa-maso-Gabas.
Marayun za su yi karatun firamare da sakandare a ita wannan makaranta, inda tuni Ministan, shine tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, ya biya kuɗin makaranta da na ciyarwar yaran gaba ɗaya.
Yanzu haka, tuni an sake ɗaukar rukuni na biyu na marayu 25, da su ka haɗa da maza 15, mata 10, ƴan shekara 6 zuwa 7, a gidan karatun da Ministan ya buɗe.
An sakawa gidan marayun sunan mahaifiyar Ministan, inda a ke baiwa yara marayu matsuguni, abinci, Ilimi, lafiya da kuma wasanni, a ƙarƙashin kulawar ƙwararrun malaman makaranta da masu kula da yara.
Shekaru 5 kenan Ya Zarah Orphans Foundation na kula da yaran da a ka kashe iyayen su sakamakon faɗan Boko Haram da sauran su.
A bikin yaye daliban a jiya Asabar a Potiskum, Abubakar, wanda kuma shine Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Ya Zarah, ya yi nuni da cewa bayan baiwa marayun kulawar da ta dace, basu ilimi kyauta na ɗaya da ga cikin manufofin gidauniyar.
Ministan, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Ilimi mai Zurfi na Jihar Yobe, Muhammed Munkaila, ya ce za a gina shaguna a bada su baya domin Gidauniyar ta samu kuɗin shiga da za ta riƙa ɗawainiyar kanta da kanta ta yau da kullum.