Majiyoyi mabambanta sun tabbatar da cewa miliyoyin mutane ke shiga sahun tattaki da maukibai mabambanta a najeriya domin kwatanta wannan sananniyar ibadar ta tattaki wacce ake gudanarwa duk shekara a karbala dake kasar Iraki.
Mutane da dama kan tambaya, shin me yasa miliyoyin zasu fito suna tattakawa a najeriya bayan asali a Iraki akeyin wannan ibada kuma ma Imam Hussaini (S.a) din da ake tattakin saboda shi ba’a najeriya aka kashe shi ba, a Iraki aka shahadantar dashi amma wasu sunzo suna wahalar da kawunan su a gida najeriya.
Iren iren masu wadannan ibhamomi sai mu ce musu ai an sani sarai cewa a Iraki ne Imam Hussain (S.a) yake amma wadannan bayin Allah da kuke gani a miliyoyi din sun fito ne domin kamantawa amma ba suna cewa Imam Hussaini din yana najeriya bane.
Da zaka bi miliyoyin masu tattakin daya bayan daya ka musu tambayar dalilin wannan tattakin da sukeyi, zasu baka amsa iri daya ne idan ma baka yi aune ba sai su baka amsa da kalmomi iri daya.
Shi tattakin najeriya da turanci ma cewa akayi ”Arbain Symbolic Treck” ma’ana kwatanta tattakin arba’in, kuma manyan malaman mazhabar shi’a sun tattabar da sahihancin sa.
Amma shi ko tattaki wanda akeyi a Iraki wannan babu wanda ya isa ya kawo ishkali a kansa domin tun zamanin sanannun sahabbai akeyi.
Sahabbai sunyi musharaka a wannan tattakin kuma tun wancan lokacin fiye da shekaru dubu kenan ana gudanar wannan ibada ta tattaki.
Ba iya ‘yan shi’a ba hatta mabiya takarkin ahlu sunnah dama kiristoci kanyi musharaka a wannan gagaruwmar Ibada ta tattaki.
A halin d ake ciki taron tattaki na karbala na zaman taro mafi yawan jama’a da ake gudanarwa a fadin duniya, wannan hakika ta tabbatar da hakan ba wai an kirkira bane wanda bai yarda ba kuma yana iya bincikawa.