Gurbin sarki ya samu ne a masarautar Kano mai dimbin tarihi yayin da a ranar 6 ga watan Yunin 2014, Allah ya yi wa mai martaba marigayi Alhaji Ado Bayero rasuwa bayan shafe shekaru 51 yana mulki.
Bisa al’ada masu zaben sarki ne za su aike wa da gwamna jerin sunayen wadanda suka bayyana sha’awarsu ko wadanda aka ayyana, shi kuma gwamna ya zabi duk wanda ya gama dama a ciki.
Masu iya magana na cewa; rabon kwado ba ya hawa sama ko ya hau ma zai sauko. Ashe rabon tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi ne ya zamo Sarkin Kano.
Ranar 8 ga watan Yuni ne Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya zabe shi don maye gurbin marigayi Alhaji Ado Bayero, kwana biyu bayan rasuwarsa.
Ko da zamowarsa Sarki wanda dama shi ne babban burinsa na rayuwa, Sanusi Lamido ya fara gudanar da sauye-sauye a wani salon shinfida mulki dan zamani.
Farawa da bukatar a kira shi da sunan Muhammadu Sanusi II, da kuma aiwatar da gyaran fadar Kano tare da yi mata ado na zamani mai kayatarwa.
Haka tafiya ta tafi har sai da mulkin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya kare Abdullahi Umar Ganduje ya gaje shi.
Da farko alaka tsakanin shugabannin biyu na tafiya daidai kafin ta koma tafiyar Agwagwa. Dangantakar ta yi tsami ce tun bayan da Sarki Sanusi ya fara sukar wasu daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Umar Ganduje kamar batun ciwo bashin biliyoyin dalar Amurka don gina jirgin kasa mai amfani da wutar lantarki.
Wannan suka dai ba karamin tasiri ta yi ba wajen dagula wa gwamtin Ganduje lissafi kasancewar sarkin ya yi ta ce a birnin Ikko kuma duk kasa baki daya ta gani.
Ba iya gwamnatin jiha kawai sukar Sarki Sanusi ta tsaya ba, hatta gwamnatin tarayya ma ba ta tsira ba, don haka ne makusanta Ganduje suka fara kitsa masa kawai ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda. Amma Ganduje ya yi taka-tsantsan saboda abin da yake shirin yi zai shiga tarihin da ba za a taba mantawa da shi ba.
Dangantaka ta yi tsami
A kowanne rikici tabbas akwai masu amfana daga cikinsa. A wannan lokacin ‘yan gaba-gaba na jikin gwamna suke kara ruruta wutar rikicin.
Kamar yadda ya fada da bakinsa a yayin wata hira da yayi da a rediyo, suna da masaniyyar cewa sarkin yana goyon bayan jam’iyyar PDP zaben 2015, wanda bai kammala ba kuma har ya je wurin shugaban kasa yana son lallai a bai wa Abba.
A cewar Ali Baba a gama lafiya mai bai wa Gwamna Abdullahi Ganduje shawara a fannin addinai.
Haka kuma a ranar wata Sallar Idi, Gwamna Ganduje ya makara amma Sarki Sanusi ya ki saurarawa ya karaso, sai a hanya gwamnan ya samu Sallar.
Daga nan, Gwamna Ganduje ya kudiri aniyar ramawa kura aniyarta, Gwamnatin Ganduje ta shirya wata sabuwar doka a karkasa masarautar Kano zuwa 5.
Daga cikin sabbin da za aka kirkiro masu daraja ta daya sun hada da: Masarautar Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi.
A cikin dokar, za a zabi shugaban majalisar Sarakunan Kano duk bayan wani lokaci, amma Sarki Sanusi ne a matsayin na farkon shugaban majalisar, sannan kuma idan shugaban ya gaza halartar zaman majilisar sarakunan ba tare da wani dalili ba har sau uku ba, to gwamna zai iya tsige shi tare da maye gurbinsa da wani.
Masu zuga sun zuga
Duk da shi ma Gwamna Ganduje na neman hanyar da zai rama laifukan da Sarki Sanusi ya yi masa, amma magana daga bakin Ali Baba ta tabbatar da cewa “duk wani wanda yake makusancin Ganduje sai da ya ce a sauke Sarki Sanusi” ko ba komai, Rabiu Musa Kwankwanso da Sarki Sanusi za su dandana. Kenan an jefi tsuntsu biyu da dutse daya.
A ranar 21 Nuwambar 2019 ne gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ya yi buris da umarnin kotu na dakatar da shi daga lissafa sabbin masarautu 5 da ya kirkira a matsayin halstattu, inda ya ci gaba da mu’amalantarsu a sha’anin mulki a matsayin halastattun sarakuna.
Daga karshe dai bayan abu ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin masarautar da Gwamnatin Kano, Gwamna Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II daga kan mulki a ranar 9 ga watan Maris 2020.
Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa da ma can Sarki Sanusin ba cancanta ba, kawai dai tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ne yake son bakanta wa shugaban kasa Jonathan rai, saboda ya tsige Sanusi Lamidon daga shugabancin gwamnan babban bankin kasa.
Abin murna a gidan Bayero
Bayyana sunan Aminu Ado a matsayin wanda zai zamo Sarkin Kano na 15, ya kasance wani babban abin farin ciki ga ahalin Bayero, domin bayan gadar mahaifin dan’uwansa ma Sarki Nasiru Ado ya zama sarki mai daraja ta daya a masarautar Bichi.
Komai na tafiya daidai har da lokacin zaben 2023, inda tsagin jam’iyyar NNPP suka zargi masarautar Kano da goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki, wanda wannan ta sanya suka fara lissafin matukar suka samu damar lashe zaben za su dauki mataki kamar yadda APC ta sauke Muhammadu Sanusi II.
Bayan kurar zabe ta lafa, NNPP ta yi nasara a zabe da kuma kotu, sai Gwmanan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatinsa ba a waiwayi maganar masarautu ba har kusan shekara guda.
DUBA NAN: ‘Yan Achaba Sun Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda A Legas
Amma akwai kishin-kishin na cewa gwamnan na son cire Sarki Aminuda kuma dawo da Muhammadu Sanusi II.