Manyan tatsuniyoyi guda hudu na Sin na nufin tatsuniyoyi hudu da aka yada baka da baka ko a rubuce kan takarda da dai sauransu a kasar Sin, wadanda suka fi yin tasiri.
Wadannan tatsuniyoyi hudu da dai sauransu sun zama wani muhimmin kashi na adabin jama’ar kasar Sin.
Dukkan tatsuniyoyin hudu sun bayyana labaran soyayya. Wannan ya bayyana amincewar jama’a ga hakikanin soyayya.
Wata mace kirar Mengjiangnv
A yayin daular Qin, akwai wata mace mai kyan gani sosai, a kan kira ta Mengjiangnv.
Ta shiga cikin soyayya tare da Fan Xiliang bayan da suka gamu da juna a karo na farko. Sai bayan samun amincewar iyayensu, su biyu sun shirya aure.
Amma a daidai wannan lokaci, sarki Qinshihuang yana share fagen gina babbar ganuwa, shi ya sa sojojinsa sun kama mutane a ko ina domin gina ganuwar.
A ranar aurensu kuma, sun cafke Fan Xiliang bisa karfi, har sun tura shi zuwa wani wuri mai nisa sosai domin gudanar da aiki. Mengjiangnv ta yi bakin ciki kwarai da gaske tare da yin fushi, tana begen mijinta sosai. A kai a kai, lokacin sanyi ya yi. Mengjiangnv ta samar da tufafin kaucewa sanyi, ta je ta nemi mijinta a babbar ganuwa.
Bayan sha wahalhalu masu dimbin yawa, Mengjiangnv ta isa babbar ganuwa a karshe. Amma a wannan wuri, ta ga ganuwa kawai a maimakon mijinta. Daga bisani, ta samu labari da cewa, Fan Xiliang ya riga ya mutu a sakamakon yawan aiki, an binne shi a kofar babbar ganuwa. Da ganin haka, Mengjiangnv ta yi kuka. Hawayenta sun yi kama da ruwan sama ba tare da kasala ba har na tsawon kwanaki uku. Hakan ya burge sararin sama da kasa, har ma ta lalata babbar ganuwa kilomita 400. Gawar mijinta ta fito daga buraguzan babbar ganuwa. A karshe ta samu damar ganinsa a karo na karshe.
Wata mace mai suna Bai Suzhen da mijinta mai suna Xu Xian
A yayin ranar Qingming ta kasar Sin, birnin Hangzhou cike yake da furanni masu launin ja da itatuwan Willow masu launin kore da tabki da duwatsu, wadanda suke da kyan gani sosai. Dodannin macizai mata biyu masu suna Bai Suzhen da Xiaoqing sun kai ziyara a wannan wuri. An yi ruwan sama. Su biyu sun gamu da wani matashi mai suna Xu Xian ta hanyar aron laima. Bai Suzhen da Xu Xian sun fada cikin soyayya. Ba da dadewa ba, sun yi aure, sun bude wani kantin sayar da magunguna tare da ba da jiyya. Suna jin dadin zaman rayuwa sosai.
Amma wani sufi mai suna Fahai dake gidan ibada na Jinshan ya tarar da lamarin, sai ya yi kokarin raba su. Da farko, ya gaya wa Xu Xian matsayin matarsa na wata dodanniyar macijiya, tare da tsara wani shiri, ta haka Bai Suzhen ta bayyana hakikanin jikinta na macijiya. Daga bisani, Fahai ya cafke Xu Xian a gidan ibadan Jinshan. Bai Suzhen da Xiaoqing sun isa gidan ibada, sun roki Fahai da ya saki Xu Xian, amma ba tare da samun nasara ba. A sabili da haka, Bai Suzhen ta haifar da ambaliyar ruwa, ta yi gwagwarmaya da Fahai. Amma sabo da ta sami ciki, shi ya sa ta sha kaye a karshe. Fahai ya karbe ta a kwanonsa na zinariya, ya dasa shi a karkashin tatsuniyar Leifeng dake dab da tabkin Xihu. A sakamakon haka, an raba masoya biyu.
Daga baya, Xiaoqing ta tsere daga gidan ibada na Qingshan, ta samu horo yadda ya kamata. A karshe, ta ci nasarar Fahai, ta tilasta masa zuwa jikin kaguwa. Sai ta ceci Bai Suzhen daga karkashin tatsuniyar Leifeng. Daga bisani, Bai Suzhen da Xu Xian sun sake yin zama tare.
A cikin wannan labari, an samar da wata dodanniyar macijiya mai kyan gani da jin tausayi, tare da nuna babban yabo ga soyayya mai kyau.
Matashi Niulang da matarsa Zhinv
An ce a zamanin da da can, akwai wani matashi mai jin tausayi dake kiwon shanu, yana fama da talauci. Wata rana, bisa taimakon wani tsohon sa, ya gamu da wata waliyin sararin sama mai suna Zhinv. Zhinv ya fada cikin soyayya da wannan matashi mai kiwon shanu, sai sun yi aure. Daga bisani, Zhinv ta haifi ‘ya’ya biyu, wato wani jariri da wata jaririya. Suna jin dadin zaman duniya.
Amma ba zato ba tsammani, mahaifin Zhinv ya yi fushi a sakamakon lamarin. Matar sarkin sararin sama mai suna Wangmu(Wangmu: wata waliyin sama ce ta zamanin da, wadda take da babban iko) ta ba da umurni ga Zhinv da ta koma fadar sama nan take. Ko da yake ba ta so ta koma ba, amma babu yadda za ta yi, sai Zhinv ta tafi ba tare da miji da ‘ya’yanta ba, ta tashi bisa gajimare. Matashi mai kiwon shanu ya yi bakin ciki, ya bi matarsa tare da ‘ya’ya biyu bisa taimakon tsohon sa. Wangmu ba ta iya hana su ba, sai ta yi amfani da fasaharta, ta samar da wani kogin taurari mai fadi a tsakaninsu.
Daga baya, Niulang da Zhinv su kan hangen juna a gabobi biyu na kogin taurari. Amma wannan ba zai rage soyayyar dake tsakaninsu ko kadan ba. A ran 7 ga watan Yuli na kowace shekara bisa kalandar noma, dubu-dubun tsuntsayen Magpie sun zo sun kafa wata gada bisa jikuna a kan kogin taurari. Sai wannan iyali na iya haduwa. A sakamakon haka, wannan rana ta kasance ranar bayyana soyayya da ba da kyauta ga masoya, ma iya cewa, wannan ne ranar soyayya ta yankin gabas. An ce a wannan rana, idan ka zauna a karkashin bishiyoyin inabi, ka yi shiru ka saurara, kana iya saurari abubuwan da suke magana a kan gadar tsuntsayen Magpie.
Liang Shanbo da Zhu Yingtai
An ce a da can, akwai wata mace mai hikima da kyan gani, sunanta Zhu Yingtai. Amma a wancan lokaci, an nuna rashin amincewa ga mata da su shiga makaranta. A kokarin samun damar koyon ilmi, Zhu Yingtai da wata yarinya mai ba da hidima sun yi adon maza, sun shiga makarantar dake birnin Hangzhou.
A wannan wuri, Zhu Yingtai ta gamu da Liang Shanbo, wanda yake da ilmi mai zurfi kana mai kirki sosai. Su biyu sun yi alkawarin zama ‘yan uwa. Akwai dankon zumunci a tsakaninsu.
Shekaru sun wuce, wa’adin karatun Zhu Yingta ya cika. Sai ta yi ban kwana da malamai ta koma gida. Amma a daidai wannan lokaci, Zhu Yingtai ta kaunaci Liang Shanbo sosai. Liang Shanbo kuma ba shi da wata masaniya. Ya nuna girmamawa ga Zhu Yingtai. Sai sun yi ban kwana da juna. Zhu Yingtai ta yi karya da cewa, tana da wata karamar ‘yar uwa. Tana so Liang Shanbo ya yi aure da ita. Daga bisani, Liang Shanbo ya kai ziyara a gidan Zhu Yingtai. Amma mahaifinta ya riga ya tilasta diyarsa da ta auri wani dan mai kudi Ma Wencai. Liang Shanbo da Zhu Yingtai sun gamu da juna sun yi bakin ciki domin rashin damar aure. Bayan da ya koma gida, Liang Shanbo ya yi bakin ciki sosai, har ya kamu da cuta. Ba da dadewa ba ya mutu a sakamakon haka.
Zhu Yingtai ba ta da karfin canza wannan lamari ba, sai ta auri Ma Wencai. A daidai ranar auren, Zhu Yingtai ta bukaci kai ziyara a kabarin Liang Shanbo domin yin addu’a. Ba zato ba tsammani, an kada iska tare da muryar tsawa. Kabarin Liang Shanbo ya bude, Zhu Yingtai ta fada a ciki tare da yin murmushi. Sai an yi rana nan take, furanni da yawa sun sheki. Liang Shanbo da Zhu Yingtai sun zama malam-bude-littafi guda biyu, sun yi zama tare.
Wannan labari sun bayyana jarumtakar matasa ta neman soyayya a zamanin da, tare da nuna rashin amincewa ga aure irin na tilastawa da burin samun rayuwa mai jin dadi.(Amina Xu daga sashen Hausa na CMG)