Wasu kwararru sun jaddada muhimmancin horas da matasa don samun basira wajen gudanar da aiki, inda suka yi nuni da cewa, ba wai samun kwararre da kuma ma’aikatan da suka cancanta ba ne, amma me za su iya gudanarwa a matsayin tawaga daya, don amfaninsu da kuma cim ma burin da kamfanin ya sa a gaba.
Daya daga cikin kwararru din kuma Shugaban Kamfanin, Hassan Umar, a jawabin sa a wani taro, a kwanan baya, ya sanar da cewa, a bisa ka’ida, irin wannan basirar da mutane ke da ita, ta isar da sako wacce kuma kamfnin ke bukata, don cim ma burinsa na dogon zango .
Ya ce, irin wannsn basirar na mayar da hankali ne kan sabbin tsare-tsare, wadanda ake zaton mutane sun samu horo akai, inda ya kara da cewa, irin wannan basirar kan bayyana yadda ka ke hulda da sauran jama’a a, a gurin aiki.
A cewar Hamza, akwai bukatar a lura da irin basirar da matasa suke da ita, tare da mahimmancin ilimi da horo da kuma kwarewarsu wajen gudanar da aiki.
A cewarsa, ko wanne irin aiki, na bukatar wadanda suka dauki mutane aiki da su ja wasu a jiki daga ciki ko daga wajen kamfanin ka, domin bai dace a kau da kai daga irin wannan basirar ta mutane ba.
Shi ma wani daga cikin kwararru mai suna, Femi Ojo, ya fayyace bambanci tsakanin basira mai saukin samu, wadda ta hada da, basirar da mutane ke da ita, suke kuma aiwatar da ita a wajen gudanar da aiki.
Sannan kuma, ya yi nuni da cewa, ba wai ko wadansu mutune ne basirarsu za ta zama daya ba, inda ya bayar da misali da cewa, a yayin da kake karancin masu basira, za ka iya fuskantar takaicin jin zafin rashin sanun mai basira wanda in har ka lura da hakan, alamun za ka iya fuskantar kalubalen ne kan kasuwancinka.
A cewarsa, idan wadanda suka dauke ka aiki sun samu horo sosai, wajen gudanar da kyakkyawar hulda da abokan cinikayya tare da cigaba da rike su don cigaba da gudanar da huldar cinikayya, wannan zai iya ba ka damar cike gibin da kake da shi a cikin kasuwancinka.
Bugu da kari, a bisa kokarinta na son horas da matasan kasar nan, mutum miliyan biyar, kan samun basira kan aiki nan da shekara biyar masu zuwa, Kungiyar Jobberman mai zaman kanta a karkashin shirin ‘Young Africa Works’ da ‘Gidauniyar Mastercard’ a kwanan baya, ta horas da matasa sama da 5,600 na tsawon kwana uku a jihar Kano kan samun basira.
Shugabar kungiyar a Nijeriya Rolake Rosiji, ta bayyana hakan a lokacin bayar da horon a Kano. Ta cigaba da cewa, horon zai kara bude kofar samun dama wajen samun damarmaki na aiki wanda kuma ya dara fiye da ilimin da aka koyar a makaranta.
Ta ce, Arewacin kasar nan na fuskantar kalubalen iri-iri, musamman kan samun ingantacen Ilimin zamani, inda ta yi nuni da cewa, hakan ya sa, ba ‘yan yankin da dama, ba sa amfana da damar a matakin duniya haka, wannan gibin na janyo ana barin matasan yankin a baya.
Wata wadda ta halarci horon ‘Fabour Christiana Ogbuagu’ ta ce, baya ga samun horo kan samun basira koyon hakan ya kara da cewa, mun samun kwarin gwiwa kan kara hazaka da kuma samun kwarin gwiwa wajen yin magana da wadanda suka dauke ni aiki.