Kungiyar Kiristocin Najeriya ta ki amincewa da zartar batun kaddamar da tsarin Shari’a a Najeriya – CAN ta ce sam hakan ba daidai bane kasancewar Najeriya kasa ce da ba ruwanta da addini.
Ta kuma bayyana bukatar a doge kan cewa ba za a tsoma batun addini cikin tsarin mulkin kasar ba Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Rev Samson Ayokunle, ya gargadi majalisar dattijai game da shigar da batu da ayyukan kowane irin addini cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Ayokunle ya ce Najeriya kasa ce da ba ruwanta da addini kuma dole ne a kiyaye hakan cikin kundin tsarin mulki.
Ya fadi haka ne lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Punch a ranar Alhamis a Jami’ar Bowen, Iwo dake Ogbomoso.
Kwamitin rikon kwarya na Majalisar Dattawa kan Kundin Tsarin Mulki na gudanar da jawabai a kan gabatar da tsarin Shari’a a shiyyoyi daban-daban na kasar.
Lamarin da ya jawo wasu kungiyoyin kiristoci a Najeriya ke sukar lamarin, ciki har da CAN. Ayokunle ya ce, “Gyarar da za a yiwa kundin tsarin mulki ita ce hanyar ci gaba idan aka yi abubuwan da suka dace.
Amma ya yi tsokacin cewa: “Idan Najeriya kasa ce da ba ruwanta da addini, to ya kamata a ga hakan a cikin kundin tsarin mulkinmu.
Dole ne mu jingine kundin tsarin mulki guda biyu da muke amfani da su yanzu, inda aka kawo batun addini da ayyukansu a cikin kundin tsarin mulki.
Ayokunle ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da na jihohi da su fifita walwalar ma’aikata a jami’o’in gwamnati da sauran manyan makarantu.
A wani labarin daban, Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce zai yiwa Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja bulala.
An ga Wike yana barazanar bulale tsohon gwamnan a cikin wani faifan bidiyo wanda ya yadu a shafukan sada zumunta, musamman Tuwita.
Gwamnan na Ribas yana mayar da martani ne ga maganganun da aka ta’allaka ga Aliyu.