Kudin da Gwamnatin tarayya ke kashewa wajan bayar da tallafin man fetur sun kai Naira Biliyan 16 kullun.
Yawan kudin da gwamnatin tarayya ke kashewa wajan samar da tallafin man fetur ga ‘yan Naya kai Naira Biliyan 16 a kullun.
Hakan na faruwane bayan da farashin dan yen man fetur a kasuwannin Duniya yayi tashin gwauron zabi.
Farashin ya kai $91.38 akan kowace gangar mai daya. Haka ya farune saboda karancin man da aka samu.
Man yayi karanci ne saboda a yanzu kamfanonu sun fara budewa da ci gaba da aiki a kasashen turai dana Amurka bayan kullesu da aka yi na tsawon lokaci saboda zuwan cutar coronavirus.
Najeriya dai na fitar da ganga Miliyan 1.8 a kullun.