Hukumomi a Jamus ranar Litinin sun nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar kin jinin Musulmai a kasar tun bayan soma yaki a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba.
“Ba a amince da duk wani hari da za a kai kan Musulmai ko addini a Jamus ba,” kamar yadda mai magana da yawun gwamnati Steffen Hebestreit ya bayyana a wani taron manema labarai a Berlin.
“Musulmai miliyan biyar da ke Jamus suna da duk wani ‘yanci na samun kariya…,” kamar yadda ya kara da cewa.
Kungiyar kawance wadda ke yaki da kin jinin Musulunci (CLAIM) a makon da ya gabata ta yi gargadi kan karuwar kyamar Musulmai a daidai lokacin da ake samun karuwar rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.
“Muna fuskantar matukar karuwar nuna wariya ga Musulmai a Jamus. Wannan wani lamari ne da ya kamata mu nuna damuwa a kai da kuma dauka da muhimmanci,” kamar yadda Rima Hanano, shugabar kungiyar ta bayyana.
Kungiyar ta CLAIM ta tara rahotanni 53 da aka samu na barazana ga Musulmai, da nuna wariya a makonni biyu da rabi da suka gabata, daga ciki har da hare-hare goma da aka kai kan masallatai.
Za a iya cewa akwai irin wadannan rahotanni da dama na kyamar Musulmai wadanda ba a bayar da rahotonsu ba, misali wadannan sun hada da maganganu da aka yi na kyamar Musulmai a shafukan sada zumunta.
Kungiyar ta CLAIM ta yi kira kan a dauki matakai masu tsauri wadanda za a yi amfani da su domin yaki da kin jinin Musulunci da kuma bayar da kariya ga wadanda lamarin ya shafa.
Source: TRT Hausa