Hotunan wankan sallah na amarya Ummi Rahab da angonta mawaki kuma jarumi Lilin Baba sun kayatar da masoyan su.
A sabuwar wallafar da angon yayi, ya saka hotunan su wurin guda 10 cike da nishadi da farinciki shi da amaryar sa.
An dai daura auren masoyan ne a tsakiyar watan Yuni da ya gabata a wani matsakaicin biki da aka yi a jihar Kano.
A wata wallafa da mawakin ango Lilin Baba yayi a shafinsa na Instagram, ya zuba zankada-zankada hotunan shi tare da kyakyawar amaryar sa jaruma Ummi Rahab.
Cike da farin ciki tare da kyalli irin na amare zukekiyar jarumar ta bayyana a hotunan. Tana sanye da atamfa mai launin bula yayin da angonata ya ke sanye da farar shadda mai dinkin babbar riga.
An dai daura auen masoyan ne a tsakiyar watan Yunin 2022 ba tare da an yi wasu jerin bidi’o’i duk kuwa da cewa angonata yana da kumbar susa.
Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab.
A wani labari na daban, alkawarin Allah ya cika a tsakanin jarumi kuma fitaccen mawaki a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu’aibu Ahmed Idris, wanda aka fi sani da Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa, jaruma Ummi Rahab.
A yau Asabar 18 ga watan Yuni, ne dubban jama’a suka shaida daurin auren manyan jaruman guda biyu.
An yi shagulgula da dama domin raya wannan rana inda amarya Ummi ta fito shar da ita saboda tsabar kyawu da haduwa.