Rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta kama wasu ‘yan daba 54 da ake zargi da yunkurin kawo cikas ga Hawan Daushe a yayin bukukuwan sallah a jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Usaini Gumel ne, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Alhamis.
“Mun kama mutane 54 dauke da muggan makamai da ke shirin kawo cikas ga bukukuwan sallah da ke gudana a sassan jihar.
“An kwato abubuwa da suka hada da wiwi, babura da wasu muggan makamai da sauransu daga hannunsu.
“Muna da bayanan sirri da ke nuna cewa wasu matasa suna taruwa da nufin kai hari a karkashin jagorancin ‘yan siyasa a jihar.
“Sun shirya kai farmaki yayin Hawan Daushe da wasu bukukuwa a jihar.
“Muna shawartar ‘yan siyasa da su gargadi magoya bayansu kan shirin kai kowane irin farmaki,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce, hadin gwiwar hukumomin tsaro sun dauki matakan tsaro da suka dace domin tunkarar duk wani da ke shirin kawo tsaiko a lokacin Hawan Daushe da bayansa a jihar.
A wani labarin na daban hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da sunayen alkalan wasan da za su busa gasar Olympics da za a fara a watan Yuli a birnin Paris na Faransa.
Hukumar ta fitar da sunayen alkalan wasa 12 daga kasashen Afrika wadanda za su wakilci nahiyar.
Cikin alkalan da ta fitar da sunayensu babu dan Nijeriya ko daya, duk da cewa kasar tana samun habbakar kwallon kafa.
Irin wannan ce ta faru ga kasar a gasar cin kofin duniya da aka yi a 2022 a Qatar.
A tattaunawar da BBC ta yi da tsohon alkalin wasa da ya kai matakin FIFA, Ibrahim Umar Fagge, kan ko me ke janyowa ana barin Nijeriya a baya.
“Akwai dalilai da dama, na farko shi ne ko da matashi ya samu damar zama alkalin wasan FIFA, ba sa iya samun horon da ya kamata wanda zai kai shi ga fara hura wasanni a matakin manyan gasa kamar kofin duniya.
“Na biyu da yawan alkalan suna da matsala ta rashin lafiya da ba sa iya kai wa ga inda ake so. Akwai kuma matsalar shekaru mafi yawa daga cikin mutanen namu tsofaffi ne.
“Bugun zuciyar su da yadda jinin ke zagaye a jikinsu akwai hatsari a bar su, su ci gaba da guje-guje.
“Na karshe shi ne a Nijeriya babu na’urar VAR da ke taimaka wa alkalin wasa,” in ji shi.
A dokar FIFA alkalin wasa ba zai busa manyan gasar da ake yi ba sai ya kware wajen amfani da VAR.
DUBA NAN: Kiraye Kirayen Gwamnonin Kano Da Kebbi A Bikin Sallah
Nijeriya dai ta jima tana samun koma baya ta fuskar gayyatar alkalan wasa domin busa wasanni a manyan gasa da ake yi a duniya.