Yayin da ake sauraran Hajji na shekarar 2023, kasar Saudiyya ta bayyana cewa, ta ba Najeriya adadin kujeru 95,000 a 2023.
Kasar Saudiyya ta dawo wa da Najeriya wasu kudaden da aka samu matsala a kansu na mahajjan bana.
A bara, kasar Saudiyya ta rage adadin mahajjata daga Najeriya saboda barkewar annobar Korona da ta addabi duniya.
Yayin da ake shirin shiga sabuwar shekarar 2023, kasar Saudiyya ta ba Najeriya adadin kujeru 95,000 na wadanda za su yi Hajjin badi.
Wannan adadi dai shine adadin da Saudiyya ta ba Najeriya a baya kafin barkwar annobar Korona a 2020.
Wannan batu na fitowa ne daga hukumomin kasar Saudiyya a cikin wata sanarwa a ranar Laraba 21 ga watan Disamban 2022.
Hakazalika, mai magana da yawun hukumar alhazai ta Najeriya, Suwaiba Ahmad ta tabbatarwa BBC Hausa wannan mataki na kasar ta Saudiyya.
A cewarta: “Saudiya ta dawo wa da Najeriya kujerun da ta saba ba ta 95, 000, wanda a baya ta rage suka koma, 45, 000 saboda matsalar annobar korona, wanda shi din ma ba mu iya cikewa ba, saboda an bayar da shi a kurarren lokaci.”
Saudiyya ta dage wasu dokokin aikin Hajji
A bangare guda, kasar Saudiyya ta sanar da janye wasu ka’idojin da ta gindaya na takaita shekarun mahajjata, wanda aka fara kakabawa ‘yan kasashen waje a shekarar da ta gabata.
A nata bangaren, hukumar NAHCON mai kula da jigilar mahajjata ta ranar Talata ta ce, kasar Saudiyya ta dawo wa da Najeriya wasu kudaden da suka kai Riyal 542,033 (N107,864,567).
An dawo da kudaden abinci ga mahajjatan Najeriya Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, kudaden da Saudiyya ta dawo dasu na abincin da aka samu matsala ne da kamfanin Mutawwaifs mai kula da abincin mahajjata ‘yan nahiyar Afrika.
Wannan dawo da kudi na zuwa ne bayan da wasu mahajjatan Najeriya suka yi korafi kan rashin samun wadataccen abinci a lokacin aikin Hajjin bana.
NAHCON ta ce, da zarar kudin shigo hannu, za ta mika su ga hukumomin jin dadin alhazai na jihohi don rabawa wadanda lamarin ya shafa.
A hajjin shekarar 2022 da ya gabata, kasar Saudiyya ta ba Najeriya kujeru 60,000 ne kacal, saboda annobar Korona, an rage adadin.