Gwamnatin Habasha ta sanar da yin afuwa ga wasu manyan fursunonin siyasa ciki har da manyan ‘yan tawayen TPLF na yankin Tigray, a wani yunkuri na karfafa shirin babban taron warware matsalolin kasar.
Daga jerin wadanda gwamnatin Habasha ta yi wa afuwa dai, akwai fitattun myakan kungiyar TPLF da kuma shugabannin ‘yan adawa na Oromo, kabila mafi girma a Habasha, da kuma na yankin Amhara.
Sai dai, babu karin bayani kan ko an fara sakin mutanen da aka yi wa afuwar siyasar.
Firayim Minista Abiy Ahmed da ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, wanda kuma ya je fagen fama a watan Nuwamban da ya gabata don jagorantar dakarunsa a yaki da ‘yan tawayen kasar, shi ma ya yi kira da a yi sulhu da hadin kai, a cikin wata sanarwa da ya fitar yayin bikin Kirsimeti.
A wani labarin na daban Majalisar Dinkin Duniya ta ce, wani hari ta sama da aka kai kan wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankin Tigray na arewacin kasar Habasha, lamarin da yayi sanadin mutuwar ‘yan gudun hijirar Eritrea 3, ciki har da kananan yara 2.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi, ya tabbatar da kashe ‘yan gudun hijirar kasar ta Eritrea uku.
Majalisar Dinkin Duniya dai ba ta fayyace ko su waye suka kaddamar da hare-haren ta sama ba, amma gwamnatin Habasha ce kadai ke ikon shawagi da jiragen yakinta a yankin.
Zuwa lokacin wannan wallafa gwamnatin Habasha ba ta ce komai akan harin ba, sai dai a baya gwamnati ta musanta harin da aka kai kan fararen hula.
Akalla mutane 146 ne suka mutu yayin da wasu 213 suka jikkata a hare-haren jiragen yaki ta sama a yankin Tigray tun daga ranar 18 ga watan Oktoba, a cewar wata takarda da hukumomin agaji suka fitar tare da mikawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.