Wani babban Basarake, Onijagbo na Ijagbo a ƙaramar hukumar Oyun ta jihar Kwara, Oba Salawudeen Fagbemi Obembe II, ya riga mu gidan gaskiya.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Oba Fagbemi ya kwanta dama ne ranar Litinin, 5 ga watan Disamba, 2022 yana da shekaru 110 a duniya.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya jajantawa al’ummar masarautar Ijagbo bisa rasuwar Sarkinsu, Oba Fagbemi.
Sakon ta’aziyyar mai girma gwamnan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren watsa labaransa, Rafiu Ajakaye.
“Muna miƙa sakon ta’aziyya ga majalisar Sarakunan Oyun, al’ummar Ijagba da iyalan marigayi mai martaba Sarki.
Muna kuma miƙa ta’aziyya ta musamman ga Yarima Lateef Fagbemi da ‘yan uwansa bisa wannan rashi.”
“Marigayi Sarki ya kasance mutum mai hikima, hakuri da soyayyar mutanensa. Bawan Allah ne mai kokarin bauta masa, dukkanin mutane zasu yi matuƙar keqarsa.”
Gwamna AbdulRazaq ya roki Allah SWT ya sa Aljannatul Furɗausy ta zama makoma ta karshe ga Marigayi sarkin.
“Muna Rokon Allah mai girma da ɗaukaka ya sa Al-jannatun Firadus ta zama makoma ga Basaraken kuma ya baiwa iyalansa da baki ɗaya al’ummar yankin Masarautarsa hakurin jure wannan gibi.”
A cewar gwamnan cikin sanarwar da Sakataren watsa labaransa ya fitar.
Source:LegitHausa