An bizne gawar sarki Ohinoyi na kasar Ebira, Alhaji Ado Ibrahim a yammacin Lahadi a mahaifarsa, Okene, jihar Kogi.
An bizne gawar ne kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin karfe 8:40 na dare.
Gwamna Bello na jihar, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Sarkin yayin da ya kai ziyara zuwa kabarin mamacin, kuma ya yi Addu’a Allah ya gafarta wa sarki Ohinoyi kurakuransa.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, sarkin mai daraja ta daya ya rasu a safiyar Lahadi a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja.
Sakataren masarautar Ebira, Alhaji Salihu Sule, ya bayyana cewa ba a samu damar yin jana’izar ba da safiyar ranar, saboda kalubalen da aka fuskanta, inda ya ce, gawar ta bar Abuja a makare, sai da misalin karfe 6:45 na yamma ta isa Okene.
Sheik Salihu Ebere, babban limamin kasar Ebira wanda ya jagoranci jana’izar, ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayi Ohinoyi, ya kuma gafarta wa sarkin kurakuransa.
A wani labarin na daban kasuwannin man fetur da iskar gas na duniya na shirin sake fuskantar wani mako mai cike da kalubalen cinikayya bayan da Isra’ila ta fara kai hare-hare ta kasa a Gaza.
Tsoron hauhawar farashin danyen mai ya zama babbar barazana ga duk nahiyoyin duniya kasancewar yankin da ke samar da mafi yawancin man ne ke shirin afkawa yaki.
“Akwai damuwa ganin cewa, Gabas ta Tsakiya ke samar da kusan kashi uku na man fetur na duniya da Iran, wadda ke goyon bayan Hamas da sauran kungiyoyin rajin neman ‘yancin kai da ke yankin, Iran ta fada a karshen mako cewa, ‘kutsen na Isra’ila na iya tilasta kowa ya dauki mataki’.”
Gangar Danyen mai a kasuwar ranar Juma’a lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-hare ta kasa, farashin ya karu da kashi 3.2 bisa 100, inda farashin ya kai sama da dala 85 kan ganga guda.
Duk da cewa, har yanzun farashin bai ka kololuwar farashin da ya kai a kowanakin baya ba, inda ya kai sama da dala 90 kan kowace ganga amma dai akwai yiwuwar yakin ya yi tasiri a kasuwannin duniya.
Source LEADERSHIPHAUSA