Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya samu sarauta a jihar Kaduna, an nada shi ‘Dakaren’ Birnin Gwari.
Tinubu ya yi alkawarin shawo kan matsalolin da suka shafi tsaro, musamman a jihohin Arewa maso Yamma.
Yankin Birnin Gwari na daga cikin inda barnar ‘yan bindiga ta yi yawa, musamman cikin shekaru shida da suka gabata.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya zama basarake a jihar Kaduna, an yi masa nadi a matsayin ‘Dakaren’ Birnin Gwari ta jihar a ranar Litinin 13 ga watan Disamba, Premium Times ta ruwaito.
Tinubu ya samu rakiyar gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai da sauran jiga-jigan APC zuwa Birnin Gwari, inda suka samu tarbar sarkin garin, Zubairu Jibrin Maigwari II.
Ziyarar Tinubu a Birnin Gwari dai itace ta farko gareshi, kuma babban kira ga neman kuri’u ne ga jam’iyyar APC yayin da ta kaddamar da gangaminta na kamfen a Arewa maso Yammacin Najeriya.
|Zan magance matsalar tsaro a Kaduna, inji Tinubu Yayin ziyarar, Tinubu ya jaddada aniyarsa ta magance matsalolin tsaro a jihar, musamman a yankin Birnin Gwari da ma sauran yankunan Arewa maso Yamma a Najeriya.
Wadanda suka halarci wannan gagarumin ziyara kuma mai dimbin tarihi sun hada abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima, gwamna Atiku Bagudu na Kebbi da Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano.
Hakazalika da gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa, Simon Lalong na jihar Filato da dan takarar gwamnan APC a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, 21st Century Chronicle ta ruwaito.
Ina ne Birnin Gwari?
Birnin Gwari dai na daga cikin yankunan da ke yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan shekarun nan, an hallaka tare da dai-daita mutanen yankin da dama.
An rasa rayukan mazauna da matafiya masu wucewa ta yankin, an lalata gidaje bila-adadin cikin kasa da shekaru shida da suka gabata.
Ya zuwa yanzu dai an samu lafawar hare-hare a yankin kasancewar ayyukan sojin Najeriya na kara haifar da da mai ido; an kama tare da hallaka ‘yan bindiga da yawa a yankin.
Tinubu ya roki jama’ar Kaduna da su kada masa kuri’a a zaben 2023, ya san yadda zai shawo matsalar tsaro a matsayin shugaban kasa.