An umurci shugabannin Nijeriya da su daina salon rayuwa irin ta ikirari da alfahari da suke yi, su yi aiki tukuru don ganin sun tsamo masu kananan karfi daga cikin mawuyaciyar rayuwa da suke ciki.
Shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) kuma Sarkin Musulmi, Mai Martaba Muhammad Sa’ad Abubakar (III), ne ya yi wannan kiran a jiya a sakon Babbar Sallah da ya yi ga ‘yan Nijeriya.
Sarkin Musulmin, wanda ya bayyana cewa Nijeriya na cikin tsaka mai wuya ta kowane fanni duba da irin kalubalen da kasar ke fuskanta, ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran sabbin shugabanni da su yi duk mai yiwuwa cikin gaggawa domin saukakawa talakawan Nijeriya kan halin da suke ciki.
Mai Martaba, a cikin wata sanarwa da babban sakatarensa Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya fitar domin taya al’ummar musulmi murnar sallar Eid-el-Kabir, ya bayyana damuwarsa kan yadda talakawan Nijeriya ke ci gaba da fama da tsadar rayuwa ta hanyar hauhawar farashin kayayyaki.
A karshe, Sarkin ya nemi al’ummar Nijeriya – Musulmai da kiristoci da su hada kai don tabbatar da zaman lafiya da habaka tattalin arzikin kasa.