1. Malam wai ance har yanzu ana cinikin baayi?
GUMI: To ga kudi na a sayo mun bawa namiji.
2. Malam ka yi ridda!
GUMI: Ashhadu anlaa’ilaaha_IllalLah, wa’anna Muhammadan-rasululLah.
Shin na dawo? To mu cigaba.
3. Malam ka turo wani da chek ya amsa maka kudi a banki,
GUMI: wa?! Gaskiya ni ban tuamma mun bata masa lokaci, ka yi hakuri yanzu zamu sallame shi.ro kowa ba, amma kar ku bashi kudin, kuma kar ku fada mun sunan shi, banso na sanshi, kuma ku sallame shi ya tafi!
4. Malam lokacin da jirgi ya samu matsala a sama, a cikin duk fasinjoji kai kadai ne baka kidime ba, kuma ka cigaba da karanta littafin dake hannun ka, shine abun ya bamu mamaki.
Shin Malam mene lakanin?
GUMI: To yanzu in tambaye ku mana, yanzu da kuka taka doron kasa shine kuka tsere wa kamun Allah?
5. Idan suka mai tambaya ko suka so su kawo mas’ala mai rudani, sai ka ji yace, “Atai ayi karatu”
6. GUMI: Duk lokacin Karatun Sahihul-Bukhari ya kan ce; “Karatun Hadisi da aiki da shi, shine Zaman Lafiya ga Musulmai”
Malam GUMI ya rasu ranar Juma’a, 11th Ga watan Satumba, 1992. ~Malam Nasir Ahmad
Allah Ya jikansa da sauran Malaman musulunci Amin