A yau ne za’a gurfanar da basaraken jihar Oyo Solomon Akinola bisa zargin hannu a ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Za’a gurfanar dashine tare da wasu hakimansa 10 wanda aka bayyana sunayensu da Sunday Aderinto, Samson Ogunmola Timothy Adewale Aderinto, Jimoh Asimiyu, Segun Gbadebo da kuma Oluwole Ogundeji.
Sauran sune Akintaro Mathew Piamo, Rafiu Ganiyu, Adejare Adeleru and Zacheus Adeleru.
Shugaban ‘yansandan Najeriya ne ya gabatar ds kara bisa zargin da ake musu.
Daily post tace cikin abinda ake zarginsu dashi akwai garkuwa da mutane.