Abin da dokar ta-ɓaci kan samar da abinci ke nufi ga talakan Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, ya ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci a matsayin martani ga hauhawar farashin abinci a kasar.
Dele Alake, mashawarcin shugaban ƙasar kan ayyuka na musamman ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.
A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya na kokawa kan hauhawar farashin kayan abinci, kuma a yayin da ake ci gaba da kokawa, gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya ƙara jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.
Me dokar ta-ɓaci kan samar da abinci ke nufi, da tasirinta?
Da yake magana da BBC, masanin tattalin arzikin Najeriya, Bismarck Rewane ya ce ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci na nufin gwamnati ta gano kuma ta amince da lamarin hauhawar farashin kayayyakin abinci wanda ya yi muni da kuma daukar matakan warware su.
“Dokar ta-baci kan samar da abinci wani yanayi ne wanda ke buƙatar matakan warwarewa ta gaggawa. Don haka ana ayyana dokar ta-baci a kan samar da abinci saboda hauhawar farashin kayan abinci, hanyar samun kayan abinci ya ragu” in ji shi.
Masanin tattalin arzikin ya ce farashin canjin kudi a halin yanzu zai yi tasiri sosai kan sa hannun gwamnatin tarayya a kan samar da abinci.
Ya shaida wa BBC cewa “hawa ko saukar darajar Naira shi ne babban matakin da zai fi shafar farashin kayayyaki a kasuwannin Najeriya.”
Da yake magana a kan yadda gwamnati za ta iya samun nasara tare da bayar da tallafi, dole ne gwamnati ta jagoranci hanyar takaita wuce gona da iri da ɓangaren kashe kuɗi.
Shi ma da yake magana da BBC, wani mai sharhi kan harkokin zuba jari, Victor Aluiyi ya yi imanin cewa idan ƙasa kamar Najeriya za ta yaƙi matsalar ƙarancin abinci yadda ya kamata, to akwai buƙatar sai ta ci nasara wajen yaƙi a kan rashin tsaro.
Ya ce tallafin gwamnatin tarayya ba zai taɓa yin tasiri ba idan har an bar rashin tsaro ya ci gaba da munana a yankin arewacin ƙasar.
Sauran masana sun goyi bayan ra’ayin Aluyi, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnati ta yi alƙawarin shigar da tsarin tsaro don kare gonaki da manoma
saboda su iya komawa gonakinsu ba tare a wnai fargabar kai musu hari ba.
Aluyi ya ce ƴan Najeriya su yi tsammanin samun sauki da gyara a farashin abinci a makonni masu zuwa.
“Ƴan Najeriya su yi tsammanin samun saukin a kan farashin abinci a nan gaba, ba lalle saukin ya zo nan da nan ba, watakila nan da makonni biyu masu zuwa farashin abincin zai iya sauka kaɗan.” Aluyi ya shaida wa BBC.
Halin tattalin arzikin Najeriya
Tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya na ci gaba da jefa al’ummar ƙasar cikin talauci kuma hakan yana ƙara tursasa ƴan Najeriya suna guduwa zuwa wasu ƙasashe don neman arziƙi.
A cewar bankin duniya, yayin da al’ummar Najeriya ke faɗi-tashin rage talauci tsakanin al’umma, yawan ƴan Najeriya da ke fama da talauci zai karu da miliyan 13 tsakanin shekarar 2019 zuwa 2025.
Bankin duniya ya yi hasashen tatalin arzikin Najeriya zai bunƙasa da kashi 2.9 cikin dari a kowa ce shekara tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, yana mai karawa da cewa cigaban zai iya kasancewa ne ta hanyar ayyuka, kasuwanci, da masana’antu.
Abin ta tallafin ke nufin cimmawa
Alake ya ce gwamnatin tarayya na da niyyar tura wasu kuɗaɗe daga tallafin man fetur domin inganta harkar noma.
Gwamnati ta bayyana wasu dabarun da za a aiwatar a matsayin wani ɓangare na bayar da tallafin, wasu daga cikin su sun hada da:
- Gaggauta bayar da taki da hatsi ga manoma da gidaje don rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
- Samun hadin kai cikin gaggawa tsakanin ma’aikatun noma da albarkatun ruwa don inganta noman rani da kuma tabbatar da cewa ana samar da abinci a tsawon shekara.
- Ƙirkira da tallafawa hukumar kula da kayan masarufi ta ƙasa wadda za ta yi nazari tare da ci gaba da tantance farashin abinci da kuma kula da dabarun tanadin abinci wanda za a yi amfani da shi a zaman hanyar daidaita farashin hatsi da sauran kayan abinci. Ta wannan hukumar, gwamnati za ta daidaita hauhawar farashin kayan abinci.
- Samar da matakan tsaro don kare gonaki da manoma ta yadda manoma za su iya zuwa gonakinsu ba tare da fargabar hare-hare ba.
- Hada kai da kamfononi masu samar da na’urori don share dazuka saboda manoma su iya noma cikin sauƙi.
- Inganta harkokin sufuri da wajen adana da kuma fitar da kayayyaki ta hanyar yin aiki da hukumar kwastam ta Najeriya domin kawar da matsalolin da ake fama da su wajen fitar da kayan abinci da shigowa da su daga waje da kuma sufuri tsakanin birane ta hanyar rage harajin da ake karɓa.
Mene ne zai iya zama ƙalubalen wannan tallafin?
Kalubalen da tallafin gwamnatin tarayya zai fuskanta shi ne rashin tsaro a cewar Aluyi.
Ya ce Najeriya ta yi sa’a babu munanan matsalolin na muhalli da ke barazana ga samar da abinci.
“Eh, mun samu ambaliyar ruwa a bara, amma a wannan ƙasar tamu, ba mu da manyan bala’o’i da ke yin barazana ga samar da abinci. Batun shi ne tabbatar da cewa an kwashe abinci daga inda ake nomawa zuwa inda ake bukata, sannan a magance matsalar tsaro,” inji Aluyi.
A cewarsa, idan aka magance matsalar rashin tsaro, sauran batutuwan za su zo da sauki wajen magance su.