Ƙungiyar IS a Najeriya ta saki wani bidiyo da hotuna wadanda ta yi ikirarin cewa suna nuna yadda ta kai hari a wata makarantar sojoji da ke Jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
A yayin harin, ana zargin mutum goma ne suka rasa rayukansu.
Kafafen yaɗa labarai na Najeriya sun ruwaito cewa makarantar da aka kai harin wata Kwaleji ce da ake kira Tukur Buratai Institute for War and Peace inda suka ruwaito cewa an kashe farar hula biyu.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai a kan harin ba kawo yanzu.
An buɗe cibiyar ce a watan Agustan 2020 a ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka na yaƙi da ta’addanci.
Ƙungiyar ta IS ta saki bidiyon ne a ranar 13 ga watan Janairu ta manhajar Telegram.
Wata kafar yaɗa labarai ta IS mai suna Amaq ce ta shirya bidiyon. A jiki, an yi masa take da “Mayaƙan IS a yayin da suka kai hari a Kwalejin yaƙi ta Najeriya da ke garin Buratai a Litinin din da ta gabata”.