Hadarin karamar motar boss a Afirka ta Kudu ya yi ajalin yara ‘yan makaranta da direba 12.
‘Yan makaranta 12 da direbansu a Afirka ta Kudu a ranar Larabar da ta gabata, yayin da wata karamar motar bus dinsu ta kife kuma ta kama wuta a kan wata hanya a lardin Gauteng.
Hadarin ya afku kwana guda bayan bude makarantu bayan hutun hunturu.
Wasu yara 7 sun jikkata a hatsarin, wanda ya afku a garin Merafong da ke yammacin cibiyar tattalin arzikin kasar Johannesburg.
Rahotanni sun bayyana cewa wata karamar mota kirar bakkie ta afkawa bayan karamar motar da ke jigilar yaran, lamarin da ya sa motar ta rikide ta tashi da wuta.
Jami’an ilimi da sufuri sun ziyarci wurin da hatsarin ya afku da kuma yaran da suka jikkata a wani asibiti da ke kusa da Carletonville. Shugaban gwamnatin lardin Gauteng Panyaza Lesufi shi ma ya ziyarci yaran da suka jikkata.
Kakakin sashen ilimi na Gauteng Steve Mabona ya ce 11 daga cikin yaran da suka mutu sun halarci makarantar firamare ta Rocklands yayin da yaro na goma sha biyu ya tafi Laerskool Blyvooruitsig a Carletonville.
Duba nan: Kasar Mali ta kori jakadan kasar Sweden.
“Bakkie ne ya bugi motar daliban daga baya, lamarin da ya sa motar ta kife sannan ta kama wuta,” in ji Mabona, yana mai bayyana hadarin a matsayin “mummunan hatsari.”
Dubban yara ‘yan makaranta a Gauteng sun dogara ne da kananan motocin bas masu zaman kansu don kai komo daga makarantunsu a lardin da ya fi yawan jama’a a Afirka ta Kudu. Wasu da yawa sun dogara da jigilar jama’a, gami da motocin bas na birni da tasi.