An zabi Yahya Sinwar a matsayin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas.
Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta sanar a cikin wani sako cewa, an zabi Yahya Sinwar a matsayin magajin Shahid Ismail Haniyyah, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas.
Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta ayyana Yahya Sinwar a matsayin babban jagaba kuma kwamandan farmakin guguwar Al-Aqsa tare da sanya shi a cikin jerin ta’addancin kungiyar Mossad.
Duba nan: Why Zionist regime choose Tehran to assassinate Ismail Haniyeh?
Da yawa daga cikin jami’an gwamnatin sahyoniyawan sun shelanta sakin Sinwar a mamadin sakin “Gilad Shalit” wani sojan sahyoniyawan da yan gwagwarmaya suka yi garkuwa da shi a matsayin daya daga cikin kura-kuran tarihi na wannan gwamnati a shekara ta 2011 ne dai gwamnatin Sahayoniyya a tilasce ta amince da zabin gwagwarmaya da Falasdinawan na sakin Sinwar da wasu Palasdinawa dubu daya domin sakin daya daga cikin sojojinta.
Idan dai ba a manta ba Isma’il Haniyah shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas wanda ya zo Tehran don halartar bikin rantsar da Dr. Mas’ud Pezeshkian ya yi shahada a wani harin ta’addanci da jami’an gwamnatin yahudawan sahyoniya suka kai a safiyar yau Laraba 31 Yuli 2024.
Yahya Sinwar wanda dabi’unsa na kwarjini ya firgita yahudawan sahyoniya a matakin siyasa da na soja, ya taka rawar gani wajen ci gaban gwagwarmayar Palastinawa tun bayan da aka sako shi daga gidan yari na gwamnatin mamaya a shekara ta 2011, kuma yana daya daga cikin manyan mafarkai na Isra’ila.