Kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya bayyana cewar ya matukar dora yardarsa akan dan wasan Napoli, Victor Osimhen don taimaka wa Nijeriya ta lashe gasar cin kofin Afirka na 2023 mai zuwa a Cote d’Ivoire.
Osimhen shi ne ya fi zura kwallaye a wasannin share fage inda ya jefa kwallo 10 a raga.
Ana sa rai cewa Osimhen zai taka rawar gani duba da cewa shine ya lashe kyautar gwarzon dan wasan maza a kyautar CAF a watan Disambar da ya gabata.
Peseiro kuma yana fatan Osimhen ya lashe kyautar wanda ya fi zura kwallaye a gasar.
A wani labarin na daban antabbatar da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Royal Antwerp ta kasar Belgium Alhassan Yusuf a matsayin wanda zai maye gurbin Wilfred Ndidi a cikin tawagar Nijeriya a gasar cin kofin Afrika na 2024.
Yusuf wanda tun farko yana cikin yan wasan da aka fitar na wucin gadi ta Super Eagles mai mutum 41, ana sa ran zai iske takwarorinsa a sansaninsu na Abu Dhabi, UAE a ranar Laraba.
Wannan dai shi ne karon farko da dan wasan ya samu kira domin wakiltar Nijeriya.
Ndidi ya samu rauni kafin wasan da Leicester City ta doke Huddersfield Town da ci 4-1 a ranar Litinin.

Source: LEADERSHIPHAUSA