Wani dan Isra’ila ya rataye kan jaki a cikin wata tsohuwar maƙabartar Musulmai da ke Birnin Ƙudus da nufin ɓata wa Musulmai rai.
“Wani Bayahude mai tsaurin ra’ayi ya yanka jaki a gaban maƙabartar da take kusa da ginin Golden Gate tare da rataye kan jakin a kan kaburburan Musulmai da ke wajen,” kamar yadda cibiyar kula da al’amuran Musulunci ta Waqf ta fada a wata sanarwa a ranar Laraba.
“Yin hakan mummunan wulakanci ne kan maƙabartar Musulmai mafi tarihi a Birnin Ƙudus.”
Da suke bayyana mutumin da ya aikata hakan mai shekara 35 a matsayin “mara cikakken hankali”, ƴan sanda sun ce sun kama shi ne bayan da aka ankarar da su cewa wani mutum “ya taka doka da ɗaga hankalin jama’a ta hanyar rataye kan jaki” a maƙabartar.
Hotunan da ke yaɗuwa a shafukan sada zumunta sun nuna kan jakin a rataye a jikin katangar maƙabartar, wacce ke daura da ginin Golden Gate, gini mafi tsufa a Tsohon Birni wanda kuma shi kaɗai ne aka katange shi.
Bisa ga al’adar Yahudawa za a bude kofar ginin Golden Gate ne kawai a lokacin isowar Almasihu, wanda zai shiga Birnin Ƙudus ta cikinta.
‘Yan sandan sun ce mutumin yana dauke da gatari a lokacin da aka kama shi, inda suka ƙara da cewa wani da ake zargin ya taimaka wajen kai shi can ma yana tsare.
Tsokana
Makabartar dai tana kusa da harabar Masallacin Ƙudus, wuri ne mai tsarki ga Musulmai da Yahudawa, kuma wuri ne da ake zaman zullumi tsakanin Falasdinawa da Isra’ilawa.
Harabar, wadda kuma a nan Masallacin Ƙudus yake, shi ne wuri mafi tsarki a Musulunci bayan Makka da Madina a Saudiyya. Yana daga saman Bangon Yamma, wuri mafi tsarki inda aka ba Yahudawa damar yin addu’a.
A cikin ‘yan shekarun nan Yahudawan masu tsattsauran ra’ayi sun kai ziyara sau da dama a harabar, lamarin da ya fusata Falasdinawa da ke kallon hakan a matsayin tsokana.
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa Hamas ta ce aniyar kare Ƙudus ne babban dalilin da ya sa ta kai Isra’ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba.
Isra’ila ta kai wani gagarumin farmakin soji a Gaza bayan harin da aka kai ta kan iyaka, inda ta kashe Falasdinawa akalla 21,110, galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu 55,243, a cewar hukumomin lafiya na yankin.
Source: TRTHausa