Wata Babbar Kotun Majistare a Jihar Kano a Nijeriya ta aike da matar nan Hafsat Surajo wacce ake zargi da kashe “abokin kasuwancinta” Nafi’u Hafiz zuwa gidan yari kafin a ci gaba da shari’ar da aka fara yau Laraba.
Kotun ta sanya ranar 8 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2024 don ci gaba da sauraron karar.
An fara sauraron shari’ar Hafsat mai shekara 24 a Kotun da ke unguwar ‘Yan Kaba a birnin Kano bayan da rundunar ƴan sandan jihar ta kammala binckenta ta miƙa ta kotu.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne rundunar ‘yan sandan ta kama Hafsat bisa zarginta da kashe Nafi’u mai shekara 38, wanda ɗan Jihar Bauchi ne a gidan mijinta da yake Unguwa Uku bayan wata hatsaniya da ta faru tsakanin su.
Tun da fari gabanin zaman kotun ne rundunar ƴan sandan ta ce ta gurfanar da wacce ake zargin tare da sauran mutanen da ake zarginsu da taimaka mata wajen boye abin da ya faru, bayan kammala nata binciken.
“A yau 27 ga watan Disamban 2023 aka gurfanar da Hafsat Surajo a kotu kan tuhumarta da zargin kisan kai, inda mijinta Dayyabu Abdullahi da wani Mallam Adamu kuma ake zarginsu da hannu a kitsa tuggu da ɓoye gaskiya,” sanarwar ƴan sandan mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta SP Abdullahi Kiyawa ta fada.
A yayin zaman kotun, Hafsat ta amsa laifin daya cikin biyu da ake zarginta da su, wato na ƙoƙarin kashe kanta da kuma na ƙashe Nafi’u, a cewar lauyan da yake kare ta, a wata hira da gidan rediyon Freedom ya yi da shi.
“Ta amsa laifin farko na yunƙurin kashe kanta, amma ta musanta na biyu, wato na zargin kashe Nafiu,” in ji lauyan.
Labarin kisan Nafiu da ake zargin Hafsat da yi ya karaɗe shafukan sada zumunta a fadin Nijeriya, kuma batun ya ɗauki hankali sosai inda ya jawo ce-ce-ku-ce da Allah wadai daga faɗin ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa wacce ake zargi da kisan ita da mijinta iyayen gidan marigayin ne, kuma abin ya faru ne a gidansu da ke Unguwa Uku a Kano.