Sahayoniyawan sam ba mabiya addini ba ne, Shaidanu ne, su ne abin da ku musulmi kuke kira da Shaidan, inji Rabbi Yisrael David.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Kakakin kungiyar yahudawa daga birnin New York ya bayyana cewa: Mu al’ummar yahudawan mun shafe shekaru 75 ana cutar da mu da tare da Palastinawa a ayyukan yahudawan sahyoniyawa, kuma bai kamata mu dauki sahyoniyawan a matsayin wakilai na Yahudawa ba, mu gaya wa duniya don su san cewa Musulmi da Yahudawa ba su da wata matsala a tsakaninsu.
Ya kara da cewa: Ya kamata duniya ta sani cewa an yaudare su a cikin wadannan shekaru 75 da kuma labarin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta Isra’ila ta yi na nuna yahudawa da addinin yahudawa ta yaudari duniya ne kawai. kuma hakan ya haifar da rikici tsakanin musulmi da yahudawa, amma wadannan sakamakon yaudarar gwamnatin Isra’ila ne.
Sun aikata laifuffukan da ba za a amince da su ba, kuma Falasɗinawa ba za su iya yafe wa ba, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar dubun-dubatar Falasdinawa, a yanzu da kuma a cikin ‘yan makonni kadan, wannan kisa ya ci gaba da wanzuwa tsawon shekaru 75 da suka gabata, wannan labari da wannan da’awa, wajibi ne gwamnatin Isra’ila a dakatar da ita, dole ne a gano cewa karya ce, gwamnatin Isra’ila gaba daya kuma dari bisa dari wani yunkuri ne na siyasa da ke cin zarafin addinin yahudawa, ba su cancanci rayuwa a karkashin wadannan yanayin ba.
Kakakin kungiyar yahudawan Anti-Zionist ta birnin New York ya kuma bayyana cewa: Sahayoniyawan sam ba mabiya addini ba ne, Shaidanu ne, su ne abin da ku musulmi kuke kira da Shaidan.
Source: ABNAHAUSA