Mahaifiyar tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Rt Hon Yakubu Dogara, Mama Saratu Yakubu Tukur ta kwanta dama tana da shekara 103 a duniya.
A wata sanarwar da Dogara ya fitar mai dauke da sanya hannunsa a madadin iyalan mamaciyar a daren ranar Juma’a, ya ce, za a sanar da lokacin biso da mata bikin bankwana lokacin da ya dace.
Dogara wanda shine autan mamaciyar ya ce, “Muna masu kankantar da kai ga mika wuya ga ikon Allah inda muke sanar da rasa mahaifiyar mu, kaka, Mama Saratu Yakubu Tukur a ranar Juma’a 22 ga watan Disamban 2023 tana da shekara 103 a duniya.”
Sanarwar ta ce, tabbas sun shaidi marigayiyar ta yi rayuwa mai ban sha’awa da kokari wajen hidimtawa, sadaukar da kai gami da hidima wa jama’a da bauta wa Allah.
A wani labarin na daban gwamnan jiha Muhammadu Inuwa Yahaya ya ba da umarnin biyan albashin watan Disamba ga dukkan ma’aikatan jihar da takwarorinsu a ƙananan hukumomi a wani mataki na ganin ma’aikatan Jihar Gombe sun kimtsa, kuma su yi bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar shekara cikin jin daɗi da annashuwa.
Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe shine ya sananar da wannan matakin, inda gwamnan ya umarci ma’aikatar kudi ta jihar da ta tabbatar kowani ma’aikaci da ‘yan fansho sun samu albashinsu a watan Disamba a kan lokaci.
Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da kyautata jin daɗin ma’aikata ta hanyar biyan albashi da sauran haƙƙoƙinsu cikin gaggawa.
Ya na da kyau a sani cewa Jihar ta Gombe tana ci gaba da sauƙe nauyin da ya rataya a wuyanta yadda ya kamata game da haƙƙoƙin ma’aikatanta kama daga biyan albashi akan kari da kuma ci gaba da bada tallafin Naira dubu goma-goma ga kowane ma’aikaci a jihar. Wannan karimci na gwamnan yana ƙara ci gaba, yayinda a wassu jihohin ba a samun ko kwatankwacin haka.
Gwamna ya miƙa gaisuwarsa da fatan alheri ga al’ummar jihar tare da yi wa al’ummar Kirista fatan yin bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar shekara lafiya.
Source: LEADERSHIPHAUSA